Arzikin Man Fetur: Yadda Jihohi 9 Suka Samu N341bn a Watanni 6
- Jihohi masu arzikin man fetur a Najeriya sun samu makudan kudi har N341.59bn a watanni shidan farkon shekarar 2024
- A bisa tsarin mulkin kasa, ana warewa jihohi masu arzikin mai kashi 13% na rabanon albarkatun da aka hako a yankinsu
- Delta da ke Kudu maso Kudun Najeriya ce ta fi kowace jiha samun kudin, ta samu har Naira biliyan 113.87 a watanni shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An fitar da rahoto kan adadin rabano da jihohi masu arzikin man fetur suka samu a cikin watanni shida a Najeriya.
Jihohi tara masu arzikin man fetur a Kudancin Najeriya sun samu kudi har Naira biliyan 341.59 a watanni shida.
Rahoton the Cable ya nuna cewa jihohin sun samu kudin ne a watanni shidan farkon shekarar 2024 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jihohi 9 suka raba N341.59bn
1. Jihar Delta
Daga watan Janairu zuwa Yuli, jihar Delta mai arzikin man fetur ta samu kudi har Naira biliyan 113.78.
Jihar Delta ce ta fi kowace jiha samun kudin kasancewar an fi haƙo danyen mai a cikinta a tsakanin lokacin.
2. Jihar Akwa Ibom
Jihar Akwa Ibom mai arzikin man fetur ta samu kason N70.04bn a watanni shida.
Akwa Ibom ta zamo ta biyu a Kudancin Najeriya wajen samun rabano daga albarkatun man fetur.
3. Jihar Bayelsa
Bincike ya tabbatar da cewa jihar Bayelsa ta samu Naira biliyan 64.04 daga albarkatun mai da aka raba.
4. Jihar Rivers
Jihar Rivers a Kudu maso Kudu ta samu Naira biliyan 58.78 na arzikin man fetur a watanni shida.
A cikin watanni shidan, jihar Rivers ta yi fama da rikicin siyasa musamman tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike.
5. Jihar Edo
Jihar Edo ta kasance jiha ta biyar cikin wadanda suka samu rabano daga albarkatun man fetur a Kudancin Najeriya.
Edo ta samu Naira biliyan 11.90bn a tsawon watanni shida da suka wuce a shekarar 2024.
6. Jihar Ondo
Jihar Ondo a Kudu maso Yamma ta samu rabanon Naira biliyan 10.05 a cikin watanni shidan 2024.
7. Jihar Imo
Jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ta samu Naira biliyan 5.72 na rabanon albarkatun man fetur.
8. Jihar Anambra
A yankin Kudu maso Gabas, jihar Anambra ta samu rabanon albarkatun fetur har Naira biliyan 4.13.
9. Jihar Abia
Jihar Abia ita ce jiha ta karshe a cikin jihohin da suka samu rabanon albarkatun man fetur a Najeriya.
Abia ta samu rabanon Naira biliyan 3.19 a cikin watanni shidan farkon shekarar 2024 da muke ciki.
NLC ta soki karin kudin fetur
A wani rahoton, kun ji cewa yan kwadago sun yi Allah wadai da karin kudin man fetur da aka samu a Najeriya.
Kungiyar kwadago ta ce karin kudin man fetur ana cikin wahalar rayuwa a kasa zai iya jefa Najeriya a rikici.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng