'Kaduna Kun ba Mu Kunya': an Yi Cece Kuce kan Bidiyon Murnar Dawo da Wutar Lantarki

'Kaduna Kun ba Mu Kunya': an Yi Cece Kuce kan Bidiyon Murnar Dawo da Wutar Lantarki

  • Mutane sun tofa albarkacin bakinsu bayan murnar dawo da wutar lantarki a wasu jihohin Arewacin Najeriya
  • An wallafa wani faifan bidiyo da mutane ke ihu da aka tabbatar yan jihar Kaduna ne a daren jiya Laraba 30 ga watan Oktoban 2024
  • Sai dai wasu sun nuna takaici kan murnar da ake yi duk da azabtar da al'umma da aka yi fiye da kwanaki 10 saboda rashin wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Wasu mazauna jihar Kaduna sun barke da murna bayan dawo da wutar lantarki.

A daren jiya Laraba 30 ga watan Oktoban 2024 aka dawo da wuta a wasu jihohin Arewa bayan shafe kwanaki babu ita.

Kara karanta wannan

Nesa ta zo kusa: Gwamnatin Tinubu ta fadi lokacin gyara lantarkin Arewa

An barke da murna bayan dawo da wutar lantarki a Kaduna
An yi ta cece-kuce bayan wallafa bidiyon murnar dawo da wutar lantarki a Kaduna. Hoto: Transmission Company of Nigeria.
Asali: UGC

Lalacewar wutar lantarki ta durkusar da Arewa

Wani mai amfani da shafin X, @Imranmuhdz shi ya wallafa faifan bidiyo inda ake murnar dawowar wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon an gano yara da matasa na buga karafu suna ihu cewa 'NEPA ta dawo, NEPA ta dawo'.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki fiye da 10 babu wutar lantarki a mafi yawan jihohin Arewa.

Hakan ya faru ne saboda lalacewar wutar lantarki a yankin wanda ya jefa al'umma cikin mummunan yanayi.

Sai dai bidiyon da aka yada ya jawo martanin jama'a inda wasu ke cewa hakan abin takaici ne.

Wasu ko cewa suke cewa yan Kaduna sun ji kunya duk da ikirarin wayewar da ake cewa sun yi a Arewa.

Martanin mutane kan murnar dawo da wuta

@KingANAD:

"Gaskiya mutanan Kawo ba ku kyauta mana ba, kun ci amanar wayewar yan Kaduna."

Kara karanta wannan

TCN: Yadda yan bindiga suka hana gyaran wutar Arewa

@Emeka:

"Shugabannin Najeriya sun fi kowa sa'a a duniya baki daya."

@OfficialEdoOsasB:

"Tinubu yana aiki, yan Arewa kuma sai murna suke yi."

@Henryhoomen1:

"Abin takaici wannan shi ne yadda shugabanni suka mayar da mu, ya kamata an wuce maganar wutar lantarki."

@ddharunaa:

"Dawo da wutar ba zai saka mu manta da azabar da muka sha na kwanaki 10 ba, mun ba APC kuri'u amma cikin shekara 1 da kadan an wulakanta mu, shirinmu shi ne hana APC da Tinubu cin zabe a 2027."

An dawo da wuta a wasu jihohi

Kun ji cewa an dawo da wutar lantarki a wasu jihohi a Arewacin Najeriya akalla guda bakwai a daren jiya Laraba.

Hakan ya biyo bayan lalacewar wutar na tsawon fiye da kwanaki 10 saboda lalacewar turakun wuta a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.