Ma'aikata Sun Zuba Ido kan Fara Karbar Sabon Albashi, NLC Za Ta Jajubo Aiki
- Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana rashin jin dadin yadda jama'ar Najeriya ke cigaba da ninkaya a cikin wahalar rayuwa
- Kungiyar na cikin bakin ciki bayan kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya sanar da karin farashin man fetur a ranar Talatar nan
- Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero ya ce akwai yiwuwar su nemi gwamnotoci a matakin tarayya da jihohi su kara albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce ma'aikatan gwamnatin Najeriya na kara talaucewa yayin da rayuwa ke kara tsada.
Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce su na sane da yadda yan kasa ke kara nutso a cikin talauci saboda yadda tattalin arziki ya sauya.
Arise Television ta tattaro Joe Ajaero ya na cewa wahalhalun da ma'aikata ke fuskanta zai tilasta masu daukar mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai yiwuwar NLC ta nemi karin albashi
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kungiyar kwadago ta NLC ta koka game da wahalar da ma'aikata su ke ciki.
Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce su na duba mika bukatar neman karin albashi domin ma'aikata su dan sarara daga kuncin da ake sha.
Kungiyar NLC ta koka da tsadar rayuwa
Kungiyar kwadago ta kasa ta ce yan Najeriya na fama da matsanancin kalubalen rayuwa saboda matsin tattalin arzikin da kasa ta tsunduma.
Ya ce akwai bukatar a sabunta fafutuka da hanyoyin da za a kawo karshen wahalhalun da mutane ke fama da shi kafin lamari ya gama baci.
NLC ta dauki zafi kan kudin fetur
A baya mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta NLC ta yi watsi da karin farashin man fetur da kamfanin mai na NNPCL ya yi a ranar Talata, lamarin da ake fargabar zai kara tsadar rayuwa.
Kungiyar kwadago ta ce akwai yiwuwar jama'ar kasar nan su yi bore, domin talakswa ba za su iya ci gaba da jure wahalar da kudurorin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke jefa su ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng