'Ana Talaucewa,' Sanatan APC Ya Bukaci a Kara Albashi Sama da N70,000
- Tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata a APC, Adams Oshiomhole ya koka kan yadda ma'aikatan Najeriya ke kara talaucewa
- Adams Oshiomhole ya ce rashin biyan ma'aikata kudin da zai wadace su rayuwa yana iya zama barazana ga tsaron Najeriya
- Tsohon shugaban kwadagon ya bukaci a samar da madaidaicin mafi ƙarancin albashi da bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kwadago kuma Sanata a APC, Adams Oshiomhole ya koka kan albashin ma'aikata.
Adams Oshiomhole ya ce duk da an yi karin albashi amma hakan ba zai tabuka komai ga ma'aikata ba.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Oshiomhole ya yi bayani ne yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikata na talaucewa inji Oshiomhole
Jigo a APC, Sanata Adams Oshiomhole ya ce a halin yanzu kullum ma'aikata na kara talaucewa a Najeriya.
Adams Oshiomhole ya ce duk da an yi karin albashi ma'aikata sun kara shiga talauci a kan yadda suke walwala a baya.
Oshiomhole ya bukaci karin albashin ma'aikata
Sanata Oshiomhole ya bukaci gwamnati ta karawa ma'aikata albashin da ya haura N70,000, ya ce duk jihar da za ta iya ta karawa ma'aikata kudi.
Punch ta ruwaito cewa Oshiomhole ya bayyana cewa ya taba tilasata Bola Tinubu ya karawa ma'aikata kudi a kan mafi karancin albashi a lokacin da yake gwamnan Legas.
Illar ba ma'aikata albashi kaɗan
Sanata Adams Oshiomhole ya ce rashin ba ma'aikata albashi da zai wadace su zai shafi harkokin tsaron kasa.
Haka zalika ya kara da cewa idan ma'aikata ba su samun kudin da zai iya wadatar da su ba lallai tattalin arzikin kasa ya haɓaka ba.
Oshiomhole ya bukaci daidaita albashi
Adams Oshiomhole ya ce idan aka saka albashi mai yawa ma'aikata za su rasa aiki haka kuma idan ya yi kadan za su shiga matsala.
A karkashin haka, ya bukaci a samu mafi ƙarancin albashi da zai zama tsaka tsakiya ta inda gwamnati da ma'aikata ba za su cutu ba.
Abba ya kara albashin ma'aikatan Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga sahun gwamnonin da suka ayyana mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ma'aikatan jihar Kano za su rika karbar N71,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng