Matsalar Arewa Ta Fito Fili, Mahdi Shehu Ya Tona Wadanda Suka Saida Al'umma

Matsalar Arewa Ta Fito Fili, Mahdi Shehu Ya Tona Wadanda Suka Saida Al'umma

  • Mai sharhi kan harkokin gwamnati a Arewa ya caccaki yadda shugabannin yankin ke gudanar da mulki
  • Mahdi Shehu ya fusata, ya yi zargin cewa gwamnonin ba su da wata sahihiyar hanyar samar da cigaba mai dorewa
  • Ya kuma caccaki mutanen Arewa da ke karbar kudi kalilan su na sayar da kuri'arsu a duk lokutan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mai bibiyar harkokin gwamnati, Mahdi Shehu ya tona dalilin karuwar rashin cigaba a Arewacin Najeriya.

Mahdi Shehu ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Arewa ba su da wata kwakkwarar manufa ta ciyar da yankinsu gaba.

Kara karanta wannan

Dan majalisar kano ya jero illolin rashin wuta a arewa, ya ga gazawar gwamnati

Arewa
Mahdi Shehu ya caccaki yan Arewa da shugabanninsu Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

A hirar da ta kebanta da Channels Television, Mahdi Shehu ya ce gwamnoni ba sa sanya kudi a wurin da ya dace, kuma akwai alamun babu wani daftari da aka tsara na bunkasa shiyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnonin Arewa ba su da manufa:" Mahdi

Mahdi Shehu ya caccaki shugabannin Arewa wajen rashin ingantacciyar manufa da zai inganta rayuwar mazauna yanki.

Mahdi Shehu ya ce idan aka kwatanta da jagororin shiyyar na baya, sun fi na yanzu tunani mai kyau da zai cicciba yankin maimakon azurta kai.

Shugabanci: An caccaki mutanen Arewa

Mai sharhi kan harkokin gwamnati a Arewacin kasar nan, Mahdi Shehu ya dora alhakin zabar bara-gurbin shugabanni a kan masu kada kuri'a.

Ya ce tsantsar rashin tunani da bibiya ne ke sa jama'a su na zabar duk dan siyasar da ya zo da romon baka a kan farashin N1,000 ko abin da ya yi kasa da haka.

Kara karanta wannan

Rashin wutar lantarki: Yadda masu cajin waya ke samun kudade masu kauri

Gwamnonin Arewa sun mika bukata ga Tinubu

A baya mun ruwaito cewa gwamnonin Arewacin kasar nan sun mika bukatarsu ga shugaba Bola Tinubu na bukatar a gaggauta kawo karshen matsalar wutar lantarki da ta addabi yankin.

Gwamnonin yankin da sarakunan gargajiya sun tattaru a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin da shiyyar ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin da za a bi wajen magance su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.