Haske Ya Zo: Ana Murna da Aka Dawo da Wutar Lantarki a Jihohin Arewa
- Wasu daga cikin jihohin Arewacin Najeriya sun samu wutar lantarki bayan an kwashe kwanaki babu haske
- A ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024, an maido da wutar lantarki a jihar Plateau da misalin ƙarfe 7:20 na dare
- Mutane sun cika da murna yayin da suka yi arba da wutar lantarkin bayan an kwashe kwanaki 10 babu haske
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - An dawo da wutar lantarki a jihohi huɗu na Arewacin Najeriya da ke a ƙarƙashin kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JEDC).
An dawo da wutar lantarkin ne a jihohin Plateau, Bauchi, Gombe, da Benue a ranar Laraba.
Lantarki ta dawo a wasu jihohin Arewa
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an dawo da wutar lantarkin ne da misalin ƙarfe 7:20 na daren ranar Laraba, 30 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna garin Jos, babban birnin jihar Plateau sun yi ta murna lokacin da aka dawo da hasken na wutar lantarki.
A cikin kwanaki 10 da suka gabata, wasu jihohin arewacin ƙasar sun faɗa cikin duhu, bayan katsewar da layin wutar lantarki mai karfin 330kV ya yi a tsakanin jihohin Benue da Enugu.
Mutane sun yi murna
Wata mazauniyar birnin Jos mai suna Maryam Ismail ta shaidawa Legit Hausa cewa ta yi farin ciki bayan maido da wutar lantarkin.
Ta bayyana a cewa sun shiga cikin halin ƙunci sakamakon rashin wutar lantarkin da aka samu na ƴan kwanaki.
"Eh an maido da wutar lantarki a yau bayan ƙarfe 7:00 na dare. Gaskiya mun yi farin ciki sosai domin mun sha wuya sakamakon rashin lantarkin."
"Babbar matsalar da na fuskanta ta cajin waya ce inda aka tsawwala masa kuɗi ya kai har N300. Amma yanzu muna fatan an kawo ƙarshen matsalar.
- Maryam Ismail
Minista ya faɗi lokacin gyara lantarkin Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana lokacin da za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
Adebayo Adelabu ya bayyana cewa za a dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya nan da wasu kwanaki masu zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng