Yayin da Janar Lagbaja Ke Jinya a Ketare, Tinubu Ya Nada Mukaddashin Hafsan Sojoji
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an nada sabon hafsan sojojin Najeriya domin maye gurbin Laftanar-janar Taoreed Lagbaja
- Tinubu ya nada Manjo-janar, Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin mukaddashin hafsan sojojin kasar Najeriya
- Hakan ya biyo bayan cigaba da jinya da Lagbaja ke yi a Amurka na tsawon lokaci da ya fara sanya fargaba a zukatan al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin mukaddashin hafsan sojojin Najeriya.
Bola Tinubu ya amince da nadin Manjo-janar Olufemi Olatubosun Oluyede domin rike muƙamin na wucin-gadi.
Hafsan sojoji, Lagbaja na jinya a ketare
Daily Trust ta ruwaito cewa Bola Tinubu ya dauki matakin ne ganin hafsan sojoji, Laftanar-janar, Taoreed Lagbaja na cigaba da jinya a ketare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan cigaba da jinya da Lagbaja ke yi a Amurka kan rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya tabbatar da haka a yau Laraba 30 ga watan Oktoban 2024 a shafinsa na X.
Onanuga ya ce an nada mukaddashin hafsan sojojin ne domin maye gurbin Laftanar-janar, Taoreed Lagbaja kafin ya dawo.
Mukamin da mukaddashin hafsan sojoji ya rike
Kafin nadin Oluyede shi ne ke riƙe da muƙamin kwamanda na 56 a sansanin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna.
Oluyede mai shekaru 56 ya kasance ajinsu daya da Lagbaja kuma an dauke su aikin soja tare a diba ta 39.
Ya shiga aikin soja a matsayin mataimakin Laftanar a shekarar 1992, ya samu muƙamin Manjo-janar a watan Satumbar 2020.
Hafsan sojoji na cigaba da jinya a ketare
Kun ji cewa rahotanni sun ba da labarin cewa hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja yana fama da rashin lafiya.
Hakan ya sanya wasu daga cikin manyan sojoji suka fara bin kafar yan siyasa da sarakuna domin maye gurbinsa.
Sai dai rundunar sojojin ta ƙaryata labarin inda ta ce Lagbaja ya dauki hutu ne kuma babu wata matsala a shugabancinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng