Yan Bindiga Sun Ƙona Gawar Ɗan Kasuwa bayan Harbe Shi har Lahira
- Rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta tabbatar da kisan gilla da aka yi wa wani dan kasuwa mai shekaru 48, Micheal Nnaji
- Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Ohauku yayin da wasu yan bindiga suka kai masa hari da misalin karfe 9:45 na dare
- Kakakin rundunar yan sanda, DSP Joshua Ukandu ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya fadi matakin da aka dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ebonyi - Wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai mummunan hari kan wani dan kasuwa mai shekaru 48.
Rahotanni na nuni da cewa yan bindigar sun kashe dan kasuwar ne kuma suka yi masa satar kayayyaki.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa rundunar yan sanda ta ce za ta yi bincike kan lamarin domin kamo miyagun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindiga sun harbe dan kasuwa
Rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta tabbatar da cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun afka kan wani dan kasuwa mai suna Micheal Nnaji.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa yan bindigar sun kai hari ne kan dan kasuwar da misalin karfe 9:54 na dare kuma sun masa harbi biyu.
"Muna zaune a bakin shago da dare kawai sai ga wasu yan bindiga su biyu sun shigo fuskokinsu a rufe.
Suna shigowa sai suka nufi cikin gida, suka tunkari falon da Micheal Nnaji yake hutawa kuma suka masa harbi biyu.
Bayan sun karbe shi, sai suka kona gawarsa a cikin gidan kuma suka rika harbi kan mai uwa da wabi."
-Shaidar gani da ido
Bayanin rundunar yan sanda
Kakakin yan sanda a jihar Ebonyi, Joshua Ukandu ya ce za su yi cikakken bincike domin gano miyagun da suka aikata laifin.
Daily Post ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Ohauku, Ikechukwu Odono na cikin waɗanda suka halarci wajen domin duba abin da ya faru.
Sojoji sun kashe Boko Haram
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar hallaka mayakan kungiyar Boko Haram a wasu yankunan jihar Borno.
Rahotanni na nuni da cewa dakarun sojojin Najeriya sun saki wuta kan Boko Haram ne yayin da suke tsaka da wata tattaunawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng