Tsadar Rayuwa: Gwamnoni, Sarakuna na Ganawa da Tinubu

Tsadar Rayuwa: Gwamnoni, Sarakuna na Ganawa da Tinubu

  • Gwamnonin Najeriya da sarakunan gargajiya suna ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa
  • Ana hasashen cewa shugabannin suna ganawa ne domin neman mafita ga yan Najeriya kan halin da ake ciki
  • Lamarin ya biyo bayan wata ganawa da gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya suka yi ne a jihar Kaduna domin wasu matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu Tinubu yana ganawa da gwamnoni da sarakunan gargajiya.

Rahotanni na nuni da cewa shugabannin suna ganawa ne a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Tinubu
Tinubu na ganawa da sarakuna da gwamnoni. Hoto: Bayo Onanuga (An yi amfani da hoton ne domin buga misali)
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya yana cikin taron.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bukaci Sanatocin Arewa su yi watsi da wata buƙatar Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya gana da sarakuna, gwamnoni

The Guardian ta wallafa cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ganawa da gwamnonin Najeriya da sarakunan gargajiya a Aso Villa.

Lamarin na zuwa ne yayin da yan Najeriya suna yawaita kuka kan matsalolin tattalin arziki da suka yawaita a kasar nan.

Me sarakuna ke tattaunawa da Tinubu?

Duk da cewa ba a samu cikakken bayani kan dalilin zaman ba, ana hasashen cewa za su mayar da hankali ne kan wahalar rayuwa.

Ana sa ran cewa sarakuna za su ba Bola Tinubu shawara kan yadda za a rage wahalar rayuwa a Najeriya.

A ɓangaren gwamnoni, ana tsammanin za su samu bayanai da za su taimaka musu wajen kawo tsare tsare da su taimaki talaka daga wajen sarakunan.

Gwamnonin da suka halarci zama da Tinubu

An ruwaito cewa gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, gwamnan Kaduna, Uba Sani, na cikin waɗanda suka halarci taron.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnoni da sarakunan Arewa suka fadawa Tinubu, sun yi fatali da shirinsa

Haka zalika gwamnonin Taraba, Kwara, Delta Ogun da Oyo sun halarci tattaunawar a fadar shugaban kasa.

Gwamnonin Arewa sun ja da Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin Arewa sun nuna kin amincewa da dokar haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke shirin kawowa.

Gwamnonin sun bukaci Sanatocin Arewa da su yi watsi da bukatar shugaban kasar idan aka kawo ta majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng