Yan Bindiga Sun Kwace Sansanin Ɗaukar Horon Sojojin Najeriya? DHQ Ta Faɗi Gaskiya

Yan Bindiga Sun Kwace Sansanin Ɗaukar Horon Sojojin Najeriya? DHQ Ta Faɗi Gaskiya

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin cewa yan bindiga sun kwace sansanin sojoji a Kontagora a jihar Neja
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce ko inci ɗaya ƴan ta'adda ba su kwace daga hannun sojoji ba
  • Ya ce dakarun sojojin kasar Najeriya ba za su yi ƙasa a guiwa ba har sai sun ga bayan ƴan ta'adda a duk inda suka ɓuya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hedkwatar tsaro ta yi fatali da ikirarin da majalisar dokokin Neja ta yi na cewa ‘yan bindiga sun kwace sansanin horas da sojojin Najeriya da ke Kotangora.

Hedikwatar ta bayyana cewa babu ko da inci ɗaya na sansanin atisayen sojoji da ƴan bindiga suka yi gigin kwacewa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maida martani, ya ce har yanzu ƴan Arewa na tare da Shugaba Tinubu

Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba.
Hedkwatar tsaro ta musanta ƙwace sansanin horar da sojoji a jihar Neja Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Facebook

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun addabi mutane a sansanin sojoji

Tun da farko dai majalisar dokokin jihar Neja ta yi ikirarin cewa ƴan bindiga sun mamaye sansanin ɗaukar horon rundunar sojoji a Kwantagora.

Rahotann sun nuna cewa mazauna yankin sun fara tashi suna komawa wasu wuraren saboda yawan hare-haren ƴan bindiga a kauyukansu.

Hedkwatar tsaro ta musanta zargin

Da yake musanta zargin, kakakin DHQ ya ce:

"Hedkwatar tsaro ta tabbatar da cewa wannan zargin ba gaskiya ba ne, sojoji na ci gaba da fuskantar ƴan ta'adda a yankin amma babu ko inci ɗaya na sansanin ɗaukar horo da aka ƙwace."

Edward Buba ya ce dakarun sojoji sun hana da ƴan ta'adda sakat a yankin saboda yadda suke kai samame da daƙile duk wata barazanar tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka yi garkuwa da limami sun aiko sako, sun nemi N200m

Sojoji sun haɗa kai da gwamnatin Neja

A cewarsa, sojoji suna aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar Neja domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, kamar yadda Punch ta rahoto.

"Dakarun sojojinmu ba za su huta ba har sai sun kakkaɓe gaba ɗaya ƴan ta'adda a duk inda suka gudu suka ɓuya," in ji Buba.

DHQ ya bayyana wasu nasarorin sojoji

A wani labarin, kun ji cewa kamar yadda ta saba mako-mako, hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu a makon jiya.

DHQ ta ce dakarun rundunar sojoji ta yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 96, sun cafke wani kwamandan ƴan bindiga Usman Maisaje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262