Gwamna a Arewa Ya Dauki Mataki da Matashi Ya Yi Zargin Ya Kware a Neman Mata

Gwamna a Arewa Ya Dauki Mataki da Matashi Ya Yi Zargin Ya Kware a Neman Mata

  • Wani matashi ya shiga matsala bayan cin mutuncin Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue da mummunan kazafi
  • Matashin mai suna Paul Gyenger ya zargi gwamnan da kwarewa wurin neman mata. ya wallafa a shafukan sada zumunta
  • Alƙalin kotun, Kelvin Mbanongun ya umarci tsare shi a gidan kaso inda ya dage shari'ar zuwa watan Disambar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Kotun majistare a jihar Benue ta tsare wani matashi kan cin zarafin Gwamna Alia Hyacinth.

Kotun ta umarci tsare matashin mai suna Paul Gyenger kan kiran Gwamna Alia da mai neman mata.

An tsare matashi kan jifan gwamna da mummunan kazafi
Kotu ta tsare wani matashi kan zargin Gwamna Alia Hyacinth na Benue da mummunan aiki. Hoto: Alia Hyacinth.
Asali: Facebook

Matashi ya jefi gwamna da mugun zarge

The Guardian ta ce ana zargin matashin da ke rayuwa a birnin Makurdi da cin zarafi da kuma bata suna.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi rigakafi, ya nemi kotu ta shiga tsakinsa da EFCC tun kafin ya bar ofis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa Gwamna Hyacinth ya munana wurin neman mata a rayuwarsa.

Alƙalin kotun, Kevin Mbanongun bai amince da rokon da wanda ake zargin ya yi ba a gaban kotun.

Mbanongun daga bisani, ya dage cigaba da sauraran shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Disambar 2024.

Matashi ya wallafa mununan kalamai ga gwamna

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, sifeta Godwin Ato ya ce an kawo korafi kan matashin a ranar 16 ga watan Oktoban 2024.

Ato ya ce mai tsaron gwamnan, ASP Ver Ingyatu shi ya shigar da korafi a bangaren laifuffukan yanar gizo.

Mai korafin ya ce matashin ya yi munanan kalamai a cikin yaren Tivi a shafin Facebook da sunan Terna Sunday To.

Ya ce ya danganta Gwamna Alia Hyacinth da kwarewa matuka wurin iya neman mata ta kowace hanya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi, ya bada umarnin rufe makaranta bayan mutuwar wani ɗalibi

Ciyamomin ƙananan hukumomi sun yi hatsari

Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa ciyamomin kananan hukumomi uku ne suka gamu da hatsari da baburansu yayin zuwa ofis.

An tabbatar da cewa hakan ya faru ne saboda rashin samun ababan hawa a hukumance daga gwamnatin jihar Benue.

Hakan ya biyo bayan shigansu ofis tun a farkon watan Oktoban 2024 ba tare da motoci ba inda suka koma amfani da babura.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.