Sanatan APC Ya Yi Fito Na Fito da Manufar Tinubu, Ya Soki Sabon Shirin Haraji

Sanatan APC Ya Yi Fito Na Fito da Manufar Tinubu, Ya Soki Sabon Shirin Haraji

  • Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya ce ba zai zuba idanu ana kara bullo da manufofin da za su gallazawa talakawa ba
  • Ali Ndume ya nuna adawa karara da shirin gwamnatin Najeriya na kara kudin haraji n VAT daga shekarar 2025 zuwa 2029
  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana shirinta na kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10% daga yanzu zuwa shekarar 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume ya fusata da kokarin Kara kudin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ke kokarin yi.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa kan dokar harajin Tinubu da gwamnonin Arewa ke yaƙa

A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta ce ta na shirin kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 10% nan zuwa shekarar 2025.

Tinubu
Sanata ya soki shirin kara haraji Hoto: Sen Muhammad Ali Ndume/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A hirar da Sanata Ali Ndume ya yi da tashar Arise Television ya ce karawa talakawa haraji zai kara ta’azzara wahalar rayuwa da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya yi fatali da kara harajin VAT

Jaridar The Cable ta wallafa cewa tsohon mai tsawatarwan ya ce zai yaki duk wani shiri na kara haraji da zai kara takurawa talakawan Najeriya.

Sanata Ali Ndume ya fadi haka ne yayin da ake so majalisa ta amince da karin harajin VAT zuwa 12.5% daga shekarar 2026-2029.

VAT: Sanata ya ba da shawara kan haraji

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya shawarcin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan hanyar da za ta bi wajen samun karin haraji ba tare da an takurawa talakawa ba.

Kara karanta wannan

Dan majalisar kano ya jero illolin rashin wuta a arewa, ya ga gazawar gwamnati

Sanata Ndume ya ce shawarci gwamnati ta yi abin da ya dace wajen karbar karin haraji daga masu kudin Najeriya, ba wai kara tatse talakawa ba.

Gwamnati za ta kara haraji

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce akwai shirin da ta ke yi na kara karbar haraji daga yan Najeriya a shekarar 2025 duk da a baya ta karyata labarin.

Ministan kudi da tattalin arziki ya bayyana haka a taron masu zuba hannun jari da ya gudana a Amurka, amma ya ce ba kowane kaya da ake saye da sayarwa za a karawa harajin ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.