Fetur: 'Yan Kasuwa Sun Maidawa Dangote Amsa, Sun Fadi Halin da Kasuwa ke ciki

Fetur: 'Yan Kasuwa Sun Maidawa Dangote Amsa, Sun Fadi Halin da Kasuwa ke ciki

  • Kungiyar dillalan man fetur ta kasa, (IPMAN) ta bayyana mamakin yadda matatar Dangote ta ce an ki sayen fetur daga wurinta
  • Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ce akwai litar fetur miliyan 500 a ajiye, matatarsa na fitar da lita 650,000 kullum
  • A zantawarsa da Legit, Sakataren kudi na IPMAN, Musa Mai Kifi ya ce har yanzu matatar Dangote ba ta bada damar sayen fetur ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos Kungiyar dillalan man fetur na kasa (IPMAN) ta cika da mamakin ikirarin da matatar Dangote ta yi na cewa ta na fitar da fetur akalla ganga 650,000 a kullum.

Kara karanta wannan

Dan majalisar kano ya jero illolin rashin wuta a arewa, ya ga gazawar gwamnati

Shugaban kungiyar na kasa, Abubakar Maigandi ne ya bayyana haka bayan matatar Dangote ta ce yanzu haka ta na da gangar fetur miliyan 500 a kasa.

Dangote Industries
IPMAN ta ce har yanzu ba sa dauko fetur daga matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar IPMAN ta yi mamakin yadda shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce akwai man a jibge, amma yan kungiyar sun fuskanci matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dillalan man fetur sun ce akwai matsala

Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi ya bayyana cewa ‘ya’yan kungiyar ba su samu damar dauko fetur daga matatar ba har na tsawon kwanaki hudu.

Ya bayyana cewa yan kungiyar sun je dauko fetur a madadin NNPCL bayan IPMAN ta biya kamfanin N40bn na sayen man fetur domin sayarwa yan Najeriya.

“Dangote bai fara sayar da fetur ba:” IPMAN

Sakataren kudi na kungiyar IPMAN na kasa, Musa Yahaya Mai Kifi ya shaidawa Legit cewa har yanzu matatar Dangote ba ta sayar masu da man fetur ba.

Kara karanta wannan

Abin da Dangote ya gayawa Tinubu bayan sun sanya labule a Aso Villa

Alhaji Mai Kifi ya ce sun zauna da matatar Dangote domin IPMAN ta samu damar dakon fetur, amma har yanzu an gaza cimma matsaya.

'Dan kasuwar ya ce bai san abin da Dangote ke nufi da cewa akwai fetur a jibge ba bayan har yanzu an kasa ba su damar sayen fetur duk da tattaunawa da IPMAN ke yi da shi.

Ghana za ta sayi fetur daga Dangote

A wani labarin, kun ji cewa kasar Ghana ta ce akwai yiwuwar ta fara dauko fetur daga matatar Dangote a maimakon kashe $400m wajen dauko fetur daga Turai.

Shugaban hukumar da ke kula da harkokin fetur na Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ne ya bayyana haka, ya ce fetur da matatar ke fitarwa zai fi karfin ayi amfani da shi a Najeriya kadai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.