Wike Ya Bayyana Babban Aikin da Tinubu Ya Tura Shi Ya Yi a Abuja

Wike Ya Bayyana Babban Aikin da Tinubu Ya Tura Shi Ya Yi a Abuja

  • Ministan harkokin babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya nesanta daga batun sayar da filaye a garin Abuja
  • Nyesom Wike ya ce Tinubu bai tura shi Abuja domin ya sayar da filaye ba sai domin ya samar da ababen more rayuwa
  • Ministan ya kuma yi shaguɓe ga minisotocin da suke gabace shi a kujerar kan cewa ba su taɓuka wani abin kirki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana babban aikin da ya je yi a birnin.

Nyesom Wike ya bayyanawa mazauna birnin cewa babban burinsa shi ne inganta ababen more rayuwa a Abuja maimakon ya riƙa sayar da filaye.

Wike ya fadi aikin da yaje yi a Abuja
Wike ya ce ba sayar da filaye yaje yi a Abuja ba Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da aikin gina titin ƙauyen Pai a ƙaramar hukumar Kwali, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

‘Ba a son ranmu ba ne': Mabarata ga Ministan Tinubu da yake shirin fatattakarsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyesom Wike ya faɗi aikinsa a Abuja

Ministan ya nuna wajibcin samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar mazauna birni da yankunan karkara, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kalaman na Wike sun biyo bayan sukar da ake ta yi wa ministoci a Najeriya musamman game da rabon filaye da sayar da su.

"Bari na gaya muku, kuma ina so na faɗi a fili, kowa ya ji ni, Bola Ahmed Tinubu bai sanya ni minista domin na zo na sayar da fili a nan ba."
"Damuwarmu ita ce ababen more rayuwa, ababen more rayuwa, ababen more rayuwa, da ababen more rayuwa. Ko a cikin birni ne? Ko a yankunan karkara ne?"
"Wasu daga cikin waɗanda suka samu damar zama minista a nan, masu jin haushi a yanzu, masu iƙirarin suna son ku, ku tambaye su, me ya faru lokacin da suke minista? Shin sun zo yankunan karkara? Shin kun gansu?

Kara karanta wannan

Yan sanda sun fadi abin da ya jawo gini ya rufta kan mutane masu yawa a Abuja

- Nyesom Wike

Tinubu: Wike ya nemi alfarma wajen ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban kasa, Bola Tinubu addu’a.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ɗan PDP ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na da niyya mai kyau ta inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng