Muhimman Abubuwa kan Dokar Harajin Tinubu da Gwamnonin Arewa ke Yaƙa

Muhimman Abubuwa kan Dokar Harajin Tinubu da Gwamnonin Arewa ke Yaƙa

  • A farkon watan Oktoba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura buƙata ga majalisa domin neman tabbatar da wata dokar haraji
  • Dokar ta samu suka daga al'umma musamman shugabannin Arewacin Najeriya, manyan yankin su na ganin ba za a yi masu adalci ba
  • Legit ta tatttaro bayanai dalla dalla game da sabuwar dokar da shugaban kasar ke son kawowa da ta jawo suka ta ɓangarori da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Tinubu na cigaba da shan suka a kan sabuwar dokar haraji da shugaban kasa ya aika ga majalisa.

Gwamnoni da sarakunan da ke jihohin Arewa na cikin waɗanda suka soki sabuwar dokar inda suka ce za ta jefa al'umma a wahala.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bukaci Sanatocin Arewa su yi watsi da wata buƙatar Tinubu

Tinubu
Bayani dalla dalla kan sabuwar dokar haraji. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Business Day ta yi wani rahoto a kan wasu muhimman abubuwa a kan sabuwar dokar harajin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimman abubuwan kan dokar haraji

1.Karin harajin VAT

A cikin sabuwar dokar, akwai bukatar kara harajin VAT daga 7.5% zuwa 15% a tsawon shekaru masu zuwa.

A shekarar 2025 za a kara harajin zuwa 10%, a 2026 za a kara shi zuwa 12.5% sai kuma a shekarar 2030 za a kara shi zuwa 15%.

2. Cire harajin VAT kan wasu kayayyaki

A cikin sabuwar dokar, akwai bukatar cire albarkatun man fetur daga cikin karin harajin da kayayyakin da aka saye su domin ayyukan jin ƙai.

Haka zalika za a cire kayan jarirai, makaman yaki na sojoji, wutar lantarki da aka samarwa tushar wuta na kasa da sauransu daga cikin dokar.

3. Harajin 27.5% ga kamfanoni

Sashen dokar ya nuna cewa za a rika karbar harajin 27.5% na ribar da manyan kamfanoni suka samu a 2025 amma za a rage shi zuwa 20% a 2026.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Ganduje ya fadawa yan Najeriya abin da ba su sani ba kan Tinubu

Dokar za ta rika aikin ne a kan manyan kamfanoni da suke iya hada hadar kudi da ya kai N20bn a shekara.

4. Harajin 4% ga kamfanoni

A karkashin dokar, za a rika karbar harajin 4% wajen manya da kananan kamfanoni a 2025 da 2026.

Za a rika karbar harajin 3% a 2027 da 2029 sai kuma 2% daga 2030 kuma za a rika amfani da harajin ne wajen dawainiyar NELFUND.

5. Harajin 5% wajen yan caca

A karkashin sabuwar dokar, za a samar da tsarin karbar harajin 5% a wajen masu gudanar da sana'o'in caca da wasanni.

Sashe na 62 na dokar ne ya tabbatar da karbar harajin a wajen dukkan masu sana'ar caca a Najeriya.

6. Harajin 5% a kan kamfanonin sadarwa

Dokar za ta samar da tsarin karbar harajin 5% ga gwamnatin tarayya wajen masu harkokin sadarwa a Najeriya.

Rahoton Punch ya nuna cewa a farkon watan Oktoba Bola Tinubu ya aike da wasika ga majalisa kan dokar.

Kara karanta wannan

Kwanaki 8 a duhu: Yadda rashin wuta ke durƙusar da kasuwanci da sana'o'i a Arewa

Sanatocin Arewa za su yaki bukatar Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Arewa sun yi watsi da dokar harajin Bola Tinubu inda suka ce ba za ta kawo cigaba a yankinsu ba.

Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa sun umarci yan majalisun tarayya na Arewa da su ki amincewa da kudirin idan aka gabatar da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng