Kotu Ta Jikawa Gwamna Aiki, Ta Hana Gwamnatin Tarayya ba Jiharsa Kudi duk Wata
- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta zartar da hukunci kan neman hana sakarwa jihar Rivers kuɗi duk wata
- Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Joyce Abdulmalik ta hana gwamnatin tarayya sakarwa jihar Rivers kasonta daga asusun FAAC
- Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsagin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule suka shigar gaban kotun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan ƙarar neman hana gwamnatin tarayya sakarwa gwamnatin jihar Rivers kuɗinta.
Kotun a hukuncin da ta yanke ranar Laraba, ta hana gwamnatin tarayya daga ci gaba da sakarwa jihar Rivers kuɗaɗe duk wata.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa alƙalin kotun, mai shari'a Joyce Abdulmalik ce ta zartar da hukuncin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta hana babban bankin Najeriya (CBN) ba jihar damar cirar kuɗi daga asusun rarraba kuɗin shiga na gwamnatin tarayya, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Majalisa ta kai gwamna ƙara a kotu
Hukuncin ya biyo bayan ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/984/24, da tsagin majalisar dokokin jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Hon. Martins Amaewhule suka shigar a gaban kotun.
Masu shigar da ƙarar dai sun buƙaci kotun da ta dakatar da ba jihar Rivers kuɗi daga asusun gwamnatin tarayya duk wata.
Sun jingina buƙatar su ne kan cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya ƙi sake gabatar musu da kasafin kuɗin shekarar 2024 kamar yadda kotu ta yi umarni.
Waɗanda ake ƙara a cikin shari'ar sun haɗa da CBN, bankunan Zenith, Access da Akanta Janar na gwamnatin tarayya.
Sauran sun haɗa da Gwamna Siminalayi Fubara, Akanta Janar na jihar Rivers, shugaban hukumar RSIEC da alƙalin alƙalai da gwamnatin jihar.
Wike ya ba Gwamna Fubara shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, shawara kan rikicin da yake faruwa a jihar.
Tsohon gwamnan na Rivers ya buƙaci magajin nasa da ya riƙa bin doka da oda domin a samun zaman lafiya a jihar da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng