Minista Ya Bankado Katuwar Matsala, An Samu Cikas a Yaki da Yan Bindiga

Minista Ya Bankado Katuwar Matsala, An Samu Cikas a Yaki da Yan Bindiga

  • Ministan harkokin yan sandan Najeriya, Ibrahim Geidam ya yi takaicin yadda ake samun rashin hadin kai tsakanin jami'an tsaro
  • Ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar domin hade kan hukumomin tsaron kasar nan domin samun nasara a kan yan ta'adda
  • Ibrahim Geidam ya ce irin wannan matsala ce za ta kara ta'azzara matsalar tsaron da Najeriya ke fama da ita a sassan kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan harkokin yan sandan kasar nan, Ibrahim Geidam ya ce akwai babbar matsala da ke hana yaki da ta'addanci.

Ibrahim Geidam, wanda tsohon gwamnan Yobe ne ya fadi haka a taron samar da hadin kai tsakanin hukumomin tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa, ya fadi abin da ya hana jihohin Arewa samun lantarki

Police
Gwamnati ba ta jin dadin rashin jin dadin rashin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro Hoto: Nigerian Police/HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Ibrahim Geidam ya ce matsalar da ake samu na kawo cikas a yaki da miyagun ayyuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsaro: Matsalar da ke kawo cikas

Jaridar Punch ta tattaro Ministan harkokin yan sanda, Ibrahim Geidam ya zargi hukumomin tsaro da kin raba bayanan sirri a tsakaninsu.

Geidam ya shawarci hukumomi tsaro su dai na kokarin yaki da rashin tsaro ba tare da su kadai ba tare da neman taimakon junansu ba.

Ministan harkokin yan sandan Najeriya ya ce rashin samun hadin kai tsakanin hukumomin tsaro zai kawo babbar barazana ga yakin da ake yi da yan ta'adda.

Ibrahim Geidam ya bayyana cewa wannan matsalar za kuma ta dakushe yunkurin maganin matsalolin tsaron Najeriya.

Hukumar tsaro ta fusata da daukar doka

A wani labarin, kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta bayyana rashin gamsuwa bisa yadda jama'ai ke daukar doka a hannunsu wajen hukunta wadanda ake zargi da laifi.

Kara karanta wannan

An bi gida gida, an kashe mutane a rikicin manoma da makiyaya

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce ana samun masu hukunta wadanda aka kama maimakon a bar wa doka ta yi abin da ya dace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.