Gwamna Ya Fara Garambawul, Ya Kori Shugaban Jami'a da Wasu Manyan Jami'ai
- Mai girma Gwamna Alex Otti ya kori shugaban jami'ar jihar Abia da ke Uturu (ABSU), Farfesa Onyemachi Ogbulu daga aiki
- Kwamishinan yaɗa labarai ya ce gwamnan ya amince da hakan ne a taron majalisar zartaswa na jihar a ranar Litinin
- Okey Kanu ya kuma sanar da naɗin Farfesa Ndukwe Okeudo a matsayin sabon shugaban jami'ar ABSU, zai fara aiki a Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abia - Gwamna Alex Otti na Abia ya sallami shugaban jami'ar jihar da ke Uturu watau ABSU, Farfesa Onyemachi Ogbulu tare da mataimakansa.
Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu, Okey Kanu, shi ne ya sanar da tsige shugaban jami'ar da yake hira da manema labarai ranar Talata.
Ya ce Gwamna Otti ya amince da sauke shugaban ABSU a wurin taron majalisar zartaswa ta jiha wanda aka yi ranar Litinin, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya naɗa sabon shugaban ABSU
Mista Kanu ya kuma sanar da naɗin Farfesa Ndukwe Okeudo a matsayin sabon shugaban jami'ar jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Haka nan kuma kwamishinan ya ce an naɗa tsohon kakakin majalisar dokoki, Agwu U. Agwu a matsayin wanda zai kula da harkokin tafiyar da jami'ar.
Sannan Gwamna Alex Otti ya naɗa sababbin mataimakan shugaba guda biyu, ƴan kwamitin gudanarwa na jami'a da sauransu.
Dalilin sauya shugabancin jami'ar Abia
Kwamishinan ya ce an yi waɗannan naɗe-naɗen ne biyo bayan amincewa da shawarwarin da kwamitin da ya ziyarci jami’ar ya bayar.
Kanu ya ce an kafa kwamitin ne domin lalubo dabaru da hanyoyin magance kalubalen da jami’ar ke fuskanta.
Ya bayyana nadin mutanen da za su rika kula da harkokin ABSU a matsayin na farko a cikin jerin gyare-gyaren da za a yi a jami’ar.
A cewarsa, dukkan waɗanda aka naɗa za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Nuwamba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Gwamna Otti zai fara biyan sabon albashi
A wani rahoton, kun ji gwamnatin Abia za ta fara biyan ma'aikatanta sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka amince da shi a ƙasar nan.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alex Otti ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashin ga ma'aikata a cikin watan Oktoban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng