Dan Majalisar Kano Ya Jero Illolin Rashin Wuta a Arewa, Ya ga Gazawar Gwamnati

Dan Majalisar Kano Ya Jero Illolin Rashin Wuta a Arewa, Ya ga Gazawar Gwamnati

  • Dan majalisar wakilan kasar nan, Hon Datti Umar Yusuf ya shiga jerin shugabannin da su ke kokawa kan matsalar wutar lantarki a shiyyarsa
  • Dan majalisar da ke wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam ya ce bai dace gwamnatin tarayya ta zuba idanu matsalar lantarki na ci gaba da kamari ba
  • Ya bayyana cewa shiyyar Arewacin Najeriya ya fada a cikin matsaloli da dama da su ka hada da durkushewar kasuwanci da asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Dan majalisa mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam, Datti Yusuf Umar ya ce lalacewar wutar lantarki a Arewa ya jawo matsaloli masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

TCN: Yadda yan bindiga suka hana gyaran wutar Arewa

A zaman majalisar ranar Talata, Hon Datti Yusuf Umar ya ce bai kamata a zuba ido rashin hasken lantarki ya na durkusar da Arewacin Najeriya baki dayanta ba.

Datti Yusuf Umar
Dan majalisar Kano ya bukaci gwamnati ta gyara lantarkin Arewa Hoto: Datt Yusuf Umar
Asali: Facebook

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dan majalisar ya ce akwai bukatar a dauki mataki a kan kamfanonin hasken wutar lantarki da hukumar kula da lantarki ta kasa (NERC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisa ta fadi illar rashin wuta a Arewa

Hon. Datti Yusuf Umar ya ce rashin wuta a shiyyar Arewa ya kassara kasuwanci da harkokin lafiya, inda ake ta tafka asara mai yawa.

Dan majalisar da ke wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam na jihar Kano ya ce matsalar ta kara jawo matsalolin tsaro da asarar rayuka.

“A gaggauta gyara wuta:” Dan majalisa

Dan majalisar Kano ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matsalar lantarki a Arewa da muhimmanci, tare da gaggauta gyara matsalar.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa, ya fadi abin da ya hana jihohin Arewa samun lantarki

Hon Datti Yusuf Umar ya ce rashin gyaran na tsawon lokaci na nuna gazawar kamfanin wutar lantarki da hukumar NERC wajen yin aikinsu.

“Yan ta’adda na kawo cikas a gyaran wuta

A baya mun wallafa cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau I Jibrin, ya ce ‘yan ta’dda ne su ka hana gyara wutar lantarkin da ya dauki lokaci a Arewa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da mazauna yankin ke kokawa kan gazawar gwamnatin tarayya da kamfanin TCN wajen gyaran wutar lantarkin da ya lalace tun a ranar 9 Satumba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.