Tsadar Lita: Farashin Fetur Ya Sake Tashi Gidajen Man Najeriya
- Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sake ƙara farashin man fetur a gidajen mai da ke ƙarƙashin kulawarsa
- A gidajen man NNPCL da ke birnin tarayya Abuja, ana sayar da litar mai a kan N1,050 saɓanin N1,030 da ake sayarwa a baya
- Wannan ƙarin farashin man fetur da kamfanin NNPCL dai ya yi shi ne na biyu a cikin makonni uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sake ƙara farashin man fetur a karo na biyu cikin makonni uku.
Farashin man fetur a gidajen man fetur na NNPCL ya koma N1,020 a Legas yayin da ya koma N1,050 a birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana sayar da man fetur a kan wannan sabon farashin a gidan man NNPCL da ke kan hanyar Arab a Bwari cikin birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya ƙara farashin man fetur
A gidan man NNPCL da ke birnin Ikeja a jihar Legas, ana sayar da man kan Naira 1,020 kowace lita, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A ranar 9 ga watan Oktoba farashin man fetur ya koma N1,030 a birnin tarayya Abuja maimakon N897 da ake sayarwa a baya, sannan ya koma N998 a Legas maimakon N885.
Menene ya jawo fetur ya tashi?
Sake tashin farashin na man fetur bai rasa nasaba da ficewar kamfanin NNPCL a matsayin dillali tsakanin ƴan kasuwa da matatar man Dangote.
Wannan ya nuna cewa kamfanin NNPCL ba zai sake cike gibin da ke tsakanin farashin matatar Dangote da wanda ake sayarwa ƴan kasuwa ba, inda kamfanin yake biyan tallafin kusan N133 a kan kowace lita.
Farashin fetur ya tashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa farashin litar man fetur ya tashi zuwa N1,200 a mafi yawan gidajen mai a birnin Kano yayin da gidajen man NNPCL ke sayar da lita kan N904.
Rahotanni sun nuna ƙarancin man ya kara tsananta a sassan ƙasar nan, masu ababen hawa sun yi dogon layi a gidajen mai musamman na NNPCL.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng