"Tinubu ba Sai Mun Mutu ba:" Tsohon Sanata Ya Koka da Manufofin Tattalin Arzikin APC
- Tsohon Sanatan Kaduna ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta sake duba yadda tsare-tsarenta su ke jijjiga yan Najeriya
- Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya ya ce dama a kan sha wahala idan za a sake fasalta tsarin tattalin arzikin kasa
- Amma ya na ganin bai kamata a ce sai duk an mutu kafin amfanin matakan su fara bayyana ba, ya shawarci Tinubu ya duba lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, , Shehu Sani ya bayyana cewa dole ne yan kasa su ji jiki matukar gwamnati na sake fasalta tattalin arziki.
Tsohon Sanatan ya ce babu kasar da ba a shan wahala idan gwamnati ta dauko aikin gyaran tattalin arziki.
A hirarsa da Arise Television, Shehu Sani ya ce wahalar da yan Najeriya ke ciki ta kai maƙura, saboda haka ya nemi a duba lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba za a so Tinubu ba:" Tsohon Sanata
Jaridar The Cable ta wallafa cewa tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya ce babu yadda za a yi jama'ar kasar nan da ke fama da kuncin rayuwa su so Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce dole shugaban ya yi hakuri da haka, domin matakan da ya ce ya na dauka wajen sake fasalta tattalin arzikin Najeriya ba su zo da sauki ba.
Sanata Shehu Sani ya nemi sauki ga talaka
Sanata Shehu Sani ya shawarci gwamnatin tarayya da cewa ba sai jama'ar kasar nan sun mutu murus ba ya kamata a fara ganin alfanun matakan da ta ce ta na ɗauka.
Haka kuma ya nemi a samar da wasu matakan gaggawa da za su samar wa talaka sauki a lokacin da gwamnati ke ci gaba da bijiro da sababbin tsare-tsare.
Tsohon Sanata ya shawarci jagororin Arewa
A wani labarin kun ji yadda Sanata Shehu Sani ya ankarar da shugabannin Arewacin Najeriya kan muhimmancin nemo yadda za a warware matsalolin yankin.
Ya mika sakonsa ne a daidI lokacin da sarakuna su ka hadu da gwamnonin yankin, tare da jami'an tsaro domin tattauna manyan kalubalen da yan Arewa ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng