Gwamna Abba Ya yi Karin Albashi a Jihar Kano, Za a Fara Biyan Ma'aikata

Gwamna Abba Ya yi Karin Albashi a Jihar Kano, Za a Fara Biyan Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga sahun gwamnonin da suka ayyana mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ma'aikatan jihar Kano za su rika karbar N71,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi
  • Gwamnan ya ce shirye shirye sun gama kammala kuma ya bayyana watan da za a fara yi wa ma'aikatan Kano karin kuɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Kano.

A yau Talata Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da lamarin bayan nazari kan rahoton kwamitin karin albashi.

Abba Kabir
Abba ya sanar da mafi karancin albashi a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan karin albashin ne a cikin wani sako da Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahu, ya bayyana sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

N71,000 ne mafi karancin albashin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da N71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Kano.

Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da haka ne a yau Talata, 29 ga watan Oktoba domin inganta rayuwar ma'aikata.

Yaushe za a fara biyan N71,000 a Kano?

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa fara biyan sabon albashin zai kasance ne daga watan Nuwamba mai kamawa.

Bayan tabbatar da hakan, Abba Kabir Yusuf ya mika godiya ga kwamitin da ya yi aikin karin mafi ƙarancin albashi a jihar.

Kudin albashin Kano ya karu

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa kudin da ake kashewa na albashi a matakin jiha duk wata zai karu da N6bn.

Haka zalika kudin zai karu a matakin ƙananan hukumomin jihar da N7bn saboda karin albashin da aka yi.

Abba Kabir Yusuf ya ce biyo bayan karin matsayi da aka yi wa malamai 20,737 kudin albashinsu zai karu da N340m.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zama na farko a Arewa da ya amince da N80,000 a matsayin sabon Albashi

An yi karin albashin ma'aikata a Ebonyi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin da zai biya ma'aikata a jihar.

Francis Nwifuru ya amince da N75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng