Mataimakin Shugaban Majalisa, Ya Fadi Abin da Ya Hana Jihohin Arewa Samun Lantarki
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya yi wa yan Najeriya bayanin halin da gyaran wuta ke ciki
- Sanata Barau ya ce ya na tattaunawa da ofishin mashawarcin Tinubu kan harkokin tsaro domin sanin inda aka tsaya a gyaran
- Tun a ranar 9 Satumba, 2024 ne yan Arewacin kasar nan ke fama da matsalar wutar lantarki, kuma har yanzu ba a kai ga gyara ta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya yi wa yan Najeriya bayani kan dalilin da ya sa aka gaza gyara wutar lantarki.
Mataimakin Shugaban majalisar ya ce ya na tattaunawa da ofishin mashawarcin Tinubu kan harkokin tsaro don sanin inda aka kwana.
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa Barau I Jibrin ya ce sun samu bayanai kan yadda gyaran layukan wutar da su ka fadi ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yan ta'adda sun hana gyara wuta" - Sanata Barau
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin shugaban majalisa, ya ce gawurtattun yan ta'adda dauke da miyagun makamai ne su ka hana gyara lantarki a Arewa.
Barau Jibrin ya ce yan ta'addan ne su ke barazana ga rayuwar injiniyoyin da ke kokarin gyara wutar da aka shafe sama da mako guda babu shi a yankin.
Halin da ake ciki kan gyaran wutar lantarki
Sanata Barau Jibrin ya ce ofishin Nuhu Ribadu, wanda ke shawartar Bola Tinubu kan tsaro ya na aiki da TCN domin dawo da wutar lantarki Arewacin kasar nan.
Kamfanin wutar lantarki na kasa (TCN) ya bayyana cewa an samu wasu bata-gari da ake kyautata zaton yan ta'adda ne sun lalata layin wuta da ke Shiroro-Mando.
Tinubu ya ba da umarnin dawo da lantarki
A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da a gaggauta gyara wutar lantarkin Arewacin Najeriya.
Wannan na zuwa sama da mako guda da lalacewar wutar lantarkin da ya jawo dimbin asara, musamman ga yan kasuwa masu tasowa a Arewacin kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng