An Gwangwaje Yar Shugaba Bola Tinubu da Matsayi, Bayanai Sun Fito
- Ma'aikatar lura da almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta ta ba yar Bola Ahmed Tinubu matsayin jakadarta
- Shugaban ma'aikatar, Muhammad Sani Idris ne ya bayyana lamarin a wata ziyara da ya kai wa yar shugaban kasar a Legas
- Folasade Tinubu-Ojo ta nuna godiya bisa karramata da ma'aikatar ta yi tare da yin fatan alheri ga Muhammad Sani Idris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rahotanni na nuni da cewa an gwangwaje yar shugaba Bola Ahmed Tinubu da wani matsayi.
Ma'aikatar lura da almajirai ta kasa ce ta nada Folasade Tinubu-Ojo matsayin wakiliya a fadin Najeriya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Folasade Tinubu-Ojo ta bayyana farin ciki da godiya bisa matsayin da aka ba ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba yar shugaba Bola Tinubu matsayi
Ma'aikatar harkokin almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta ta karrama yar Bola Tinubu, Folasade da matsayin wakiliya.
Shugaban ma'aikatar, Muhammad Sani Idris ne ya tabbatar mata da matsayin yayin wata ziyara da ya kai mata a gidanta da ke Legas.
Dalilin ba yar Tinubu mukami
Muhammad Sani Idris ya bayyana cewa sun zabo Folasade Tinubu-Ojo ne a matsayin wakiliya bisa yadda ta ke yi wa masu rangwamen karfi taimako.
Jaridar the Guardian ruwaito cewa shugaban ya ce tana taimakawa almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya.
Diyar Tinubu ta karbi sabon matsayi
Yar shugaban kasa, Folasade Tinubu-Ojo ta nuna godiya bisa karramata da aka yi da matsayin wakiliya a ma'aikatar.
"Ina matukar godiya. Lallai an karrama ni, kuma zan tabbatar da cigaba da taimakon waɗannan yaran"
- Folasade Tinubu-Ojo
Yar shugaban kasar ta kara da cewa Najeriya za ta ci moriyar tsare tsaren da Bola Tinubu ke kawowa a bangaren ilimi.
Matar Tinubu ta rabawa mata kudi
A wani rahoton, kun ji cewa matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta raba miliyoyin kudi ga mata a jihar Zamfara domin bunkasa ƙananan sana'o'i.
An ruwaito cewa mata 1,000 ne suka samu kyautar tallafin a wannan karon yayin da matar shugaban kasar ta samu wakilci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng