Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Sabon Tsarin Samar da Lantarki a Arewa
- Rashin wutar lantarki ya sanya gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu neman mafita a jihohin Arewacin Najeriya
- Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa a yanzu haka an fara ƙoƙarin samar da wutar lantarki da hasken rana a Arewa
- Adebayo Adelabu ya bayyana yadda za a tsara raba wuta a jihohin Arewa idan aka kammala shirin nan gaba kadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Gwamnatin tarayya ta fara shirin samar da wuta da hasken rana a jihohin Arewacin Najeriya.
Hakan na zuwa ne saboda yawan lalacewar tushen wutar lantarki da ake samu a Najeriya da kuma lalacewar layukan wuta.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ministan wuta, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka ga manena labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a samar da sola a jihohin Arewa
Rahoton Channels Television ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta fara shirin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a jihohin Arewa.
Ministan wuta, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka inda ya ce shirin zai taimaka wajen rage matsalolin lantarki a Najeriya.
Dalilin samar da sola a Arewa
Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ana samun hasken rana a Arewacin Najeriya da ya wuce sa'o'i goma a kullum.
Ministan wuta ya ce hakan wata hanya ce da za a yi amfani da ita domin cin moriyar albarkatun hasken rana da ke Najeriya.
Wutar sola da za a samar a Arewa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a kowace jiha a Arewa za a samar da wuta mai karfin mega wüatt 100.
A yanzu haka dai ministan wuta ya tabbatar da cewa an fara magana da yan kwangila kan yadda za a tabbatar da yiwuwar shirin.
Za a gyara wutar Arewa a kwanaki 5
A wani rahoton, kun ji cewa ministan wuta, Adebayo Adelabu ya ce nan da kwanaki uku zuwa biyar za a kammala gyaran wutar Arewa.
Adebayo Adelabu ya tabbatar da cewa a yanzu haka injiniyoyin TCN da sauran ma'aikata sun dukufa wajen ganin an gama gyaran.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng