Ma'aikatan Jami'a da Suka Shiga Yajin Aiki Sun Kawo Sharadin Komawa Ofis

Ma'aikatan Jami'a da Suka Shiga Yajin Aiki Sun Kawo Sharadin Komawa Ofis

  • Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (SSANU) ta yi fushi da yadda gwamnatin Bola Tinubu ta rike masu albashin watanni hudu
  • Shugaban kungiyar na kasa, Mohammed Ibrahim ya ce gwamnati na yi masu wasa da hankali kan inda albashinsu su ka makale
  • Kwamred Mohammed Ibrahim ya ce babu ma'aikacin da zai koma bakin aiki har sai gwamnatin tarayya ta biya su albashinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban kungiyar ma’aikatan jami’o’in kasar nan (SSANU), Mohammed Ibrahim ya shaidawa gwamnatin tarayya abin da zai mayar da su bakin aiki.

Kwamred Mohammed Ibrahim ya ce za su koma ofis ne idan jami’ansu sun ga sakon shigowar albashin da su ke bin gwamnatin kasar nan.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Ganduje ya fadawa yan Najeriya abin da ba su sani ba kan Tinubu

Abba Sani Pantami
Ma'aikatan jami'a sun fadi shardin komawa aiki Hoto: Cmr Abba Sani Pantami
Asali: Facebook

Tashar Channels ta wallafa cewa ma’aikatan SSANU sun tsunduma yajin aiki ne tun daga daren Lahadin da ta gabata saboda kin biyansu albashin watanni hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar SSANU ta ce gwamnati ta gaza

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar SSANU ta zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yi mata rufa-rufa tare da kin biya masu bukatunsu.

Kungiyar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shaida mata cewa albashinsu ya makale ne a ma’aikatar kudi, wanda ya sa su ka ga babu mafita sai dai a tsunduma yajin aikin.

SSANU za ta zauna da gwamnati

Kungiyar ma’akatan jami’o’i ta ce ta zauna da Ministocin da ke da ruwa da tsaki kan matsalar da ta sa suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Shugaban kungiyar, Kwamred Mohammed Ibrahim ne ya shaida haka, tare da bayyana cewa sai dai ba a tattauna matsalar albashin da su ke bin gwamnatin tarayya ba.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wata magana, ya roki ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa Tinubu addu'a

Ma'aikatan SSANU za su shiga yajin aiki

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar ma'aikatan jami'o'in Najeriya (SSANU) ta bayyana takaicin yadda gwamnatin tarayya ta ki biya masu bukatunsu da za su taimaka wajen aiki yadda ya dace.

Shugaban SSANU na jami'ar BUK a Kano, Mustapha Aminu ya zargi gwamnati da kin biya masu bukatun da su ka hada da inganta mafi karancin albashinsu da N50bn da aka yi alkawarin ba su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.