'Yan Bindiga Sun Kai Harin Rashin Imani, Sun Yi Wa Bayin Allah Yankar Rago
- Yan bindiga sun tare manoma a hanyar zuwa gona, sun kashe mutane a kauyen Maridi da ke ƙaramar hukumar Isa a Sakkwato
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da wasu, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda suka ɓata bayan harin
- Wani mazaunin yankin ya ce tuni suka yi wa mutum biyu daga cikin waɗanɗa aka kashe jana'iza, yanzu kuma suna shirin yi wa sauran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi wa manoma huɗu yankar rago a yankin ƙaramar hukumar Isa da ke jihar Sakkwato.
Rahotanni sun bayyana cewa har yanzun ba a ga wasu manoman ba bayan harin da ƴan bindigar suka kai ranar Litinin da ta gabata.
Wani mazaunin yankin, Surajo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust, ya ce lamarin ya auku ne a kauyen Maridi da misalin karfe 8:00 na safiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kashe manoma a Sokoto
A cewar Surajo, maharan sun yi wa manoman kwantan ɓauna, suka hallaka su a hanyarsu ta zuwa gona.
Mutumin ya ce:
"Ƴan bindigar sun shammace su yayin da suke hanyar zuwa aiki a gonakinsu, suka yanka mutum huɗu nan take, sannan suka yi awon gaba da wasu mutum huɗu.
"Kuma har yanzu akwai wadanda ba mu gani ba, ba mu sani ba ko sun gudu cikin daji ne ko kuma maharan sun haɗa sun yi garkuwa da su.”
"Tun da safe mu ka binne mutum biyu daga cikin manoman da aka kashe, yanzu kuma muna shirin binne sauran mutum biyun."
Ƴan bindiga sun harbi uba da ɗansa
Surajo Isah ya kuma bayyana cewa a makon jiya ƴan bindiga sun harbe uba da ɗansa a kauyen, rahoton Punch.
"Ɗan ya mutu nan take yayin da uban kuma har yanzu yana kwance yana jinya a asibiti," in ji shi.
Shugaban karamar hukumar Isa, Alhaji Sharifu Kamarawa ya tabbatar da kai harin da ya zanta da manema labarai.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce har yanzu bai samu rahoto a hukumance kan harin ba.
Sojoji sun samu galaba kan ƴan ta'adda
A wani rahoton kuma, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a jihohin Borno da Yobe da ke yankin Arewa maso Gabas.
Biyu daga cikin ƴan ta'addan da aka kashe a jihar Yobe, an hallaka su ne a wajen wani wurin karɓar haraji a garin Gujba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng