Tsohon Sanata Ya Yi Magana da Ya Ji Labarin Manyan Arewa Sun Yi Zama

Tsohon Sanata Ya Yi Magana da Ya Ji Labarin Manyan Arewa Sun Yi Zama

  • Shehu Sani ya ce shugabannin Arewa sun gaza fitar da hanyoyin magance matsalolin da su ka addabi yankin a baya
  • Ya fadi haka ne da gwamnoni da masu rike da sarautun gargajiya da sauran manyan Arewa su ka hallara a jihar Kaduna
  • Tsohon Sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya ce a wannan karon, ya kamata shugabannin su samar da mafita ga Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa kan babban taron gwamnoni da manyan sarakunan gargajiya da ke gudana a jiharsa.

Ya yi na’am da yadda taron ya zo a gabar da ake bukatar waiwaye kan tarin kalubalen da shiyyar Arewacin Najeriya ke fuskanta da su ka hada da tsaro da durkushewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnoni da sarakunan Arewa suka fadawa Tinubu, sun yi fatali da shirinsa

Kaduna
Sanata Shehu Sani ya shawarci shugabannin Arewa kan matsalolin Arewa Hoto: Shehu Sani/@ubasanius
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Shehu Sani ya kalubalanci jagororin yankin su tabbata an tashi daga taron da samun hanyoyin fitar da Arewa daga kangin da ta ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Sani ya ba shugabannin Arewa shawara

Tsohon Sanata Shehu Sani a bayyana gamsuwa kan yadda shugabannin Arewa su ka zauna domin nemo bakin zaren matsalolin da su ka hana 'yan yankin samun walwala.

Ya shawarci jagororim da su samar da tartibiyar hanya da za a kawo karshen matsalar tattalin arziki da tsaro da su ka hana Arewacin Najeriya ci gaba.

Tsohon Sanata ya fadi gazawar shugabannin Arewa

Sanata Shehu Sani ya ce shugabannin Arewa a baya sun gaza kawo karshen matsalolin da ke dakushe ci gaba a yankin, musamman ta fuskar zaman lafiya.

Ya ce kamata ya yi gwamnonin yankin su hada hannu da gwamnatin tarayya, da hadin gwiwa a tsakaninsu da masana'antu masu zaman kansu wajen sake gina Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun farga, sun gane dalilin da talauci ya fi ƙamari a shiyyarsu

Sanata Sani a kan rikicin zanga zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Sanata Shehu Sani ya yi tir da yadda aka samu barkewar rikici bayan fara zanga zangar adawa da manfofin gwamnatin tarayya a kasar nan.

Sanata Shehu Sani ya danganta rikice-rikicen da aka samu da cewa wani tsari ne na yunkurin kifar da zababbiyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hanyar shiga rigar zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.