'A Soke Su': Shehi Ya ba Gwamnoni Shawara, Ya Ce Yan Sa Kai Sun Hallaka Malamai

'A Soke Su': Shehi Ya ba Gwamnoni Shawara, Ya Ce Yan Sa Kai Sun Hallaka Malamai

  • Sheikh Yusuf Musa Assadus Sunnah ya ba gwamnoni shawara kan yadda za a kawo karshen rashin tsaro na ta'addanci
  • Shehin malamin ya ce ana zargin wasu yan sa-kai da barna wanda ya kamata a dakatar da ayyukansu domin yin sulhu da yan bindiga
  • Ya ce yan bindiga da dama na cewa yan sa-kai ne matsalarsu, ya kamata a gwada soke su domin gano bakin zaren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Malamin Musulunci a Najeriya ya ba gwamnatocin jihohi da na Tarayya shawara kan matsalolin ta'addanci.

Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya ce dole a soke ayyukan yan sa-kai idan ana son kawo karshen ta'addanci.

Malamin Musulunci ya yi magana kan yadda za a kawo karshen ta'addanci
Sheikh Yusuf Musa Assadus Sunnah ya ba gwamnoni shawara kan ayyukan ta'addanci. Hoto: Sheikh Yusuf Musa Assadus Sunnah.
Asali: Facebook

Ta'addanci: Assadus Sunnah ya ba gwamnoni shawara

Kara karanta wannan

'Zan dauwamar da talauci': Kwamishina a Arewa ya yi katobara, an taso shi a gaba

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da jaridar DCL Hausa da aka wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Assadus Sunnah ya ce yan sa-kai sun hallaka wasu malamai wadanda kowa ya sani ba sai ya kira suna ba.

Malamin ya ce ya kamata a soke ayyukansu musamman idan ana son yin sulhu da yan bindiga.

Assadus Sunnah ya bukaci sanya malamai a sulhu

Ya nuna damuwa kan yadda ba a saka malamai musamman yayin sulhu da yan bindiga domin ba da tasu gudunmawa.

"Abin da ya fi shi ne gwamnoni su fara dakatar da maganar yan sa-kai saboda mafi yawan yan bindiga matsalarsu kenan, idan da za ka ji abin da suke fada, matsalarsu tun farko ba jami'an tsaro ba ne ko mutanen gari, yan sa-kai ne."

Kara karanta wannan

Kusa a PDP ya soki Tinubu kan kyale Mawatalle a mukaminsa, ya fadi illar haka

"Ban ce duk ya sa-kai mutanen banza ba ne amma tun da yan bindiga sun ce su ne matsalarsu a gwada soke su a gani, a nan za a gane ko maharan da gaske suke yi."
"Ya tabbata ba zargi be ne yan sa-kai sun kashe wasu malamai saboda sun yi magana kan yadda suke hallaka wasu da ba su da hakki."

- Sheikh Assadus Sunnah

Malamin ya ce akwai wasu yan sa-kai da suke barna wanda kusan ya fi na yan bindiga ba tare da an dauki mataki kansu ba.

Assadus Sunnah ya shawarci yan bindiga

Kun ji cewa Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tura sako na musamman ga Bello Turji da sauran yan ta'adda bayan kisan Halilu Sabubu.

Malamin ya bukaci yan ta'addan da su tuba su dawo hanyar Allah duba da yadda ake kashe su, ya ce su mutuwa a layin da suke ba kyau.

Kara karanta wannan

2027: Manyan yan siyasar Arewa sun fara hada kai, suna ganawa kan tumbuke Tinubu

Sheikh Assadus Sunna ya yabawa jami'an tsaro kan irin wannan kokari da suka yi inda ya ce sun cancanci yabo na musamman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.