Gwamnonin Arewa Sun Dunƙule, An Miƙa Dabarar Magance Matsalar Lantarki ga Tinubu
- Gwamnonin Arewacin Najeriya sun shawarci Bola Ahmed Tinubu da ya duba hanyar magance matsalar wuta a yankin
- Wannan ƙunshe a cikin takardar bayan taro da gwamnonin su ka fitar a jihar Kaduna kan ƙalubalen da yankin ke ciki
- Sanarwar ta kuma nemi gwamnatin tarayya ta ɗauki manyan matakai da za su wadata Arewa da hasken wutar lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun shaidawa gwamnatin tarayya rashin jin dadin yadda matsalar lantarki ta girmama a shiyyar.
Damuwar gwamnonin na ƙunshe a cikin sanarwar bayan taro da su ka fitar bayan ganawa kan matsalolin Arewacin Najeriya a Kaduna.
Jaridar Punch ta tattaro cewa gwamnonin sun buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta kawo ƙarshen duhun da ya mamaye yankinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnoni sun nemi magance matsalar lantarki
Kafar Voice of Nigeria ta wallafa cewa gwamnonin Arewa da masu rike da sarautun gargajiya a yankin sun bayyana damuwa kan rashin wuta.
Sun shawarci shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya samar da wasu hanyoyin samar da wutar lantarki a shiyyar domin kawo karshen mawuyacin halin da rashin wuta ke jawowa.
Gwamnoni sun fadi hanyar magance rashin lantarki
Taron gwamnonin Arewa ya shawarci gwamnatin tarayya ta kara gina wasu manyan layukan lantarki tare da samar da wasu hanyoyin wadata yankinsu da hasken wuta.
Yanzu haka Arewacin Najeriya ta shafe akalla kwanaki tara ta na fama da matsanancin rashin wutar lantarki, kuma gabanin wannan, an sha fama da ƙarancinta nan da can.
Matsalar rashin wutar ta fi ƙamari a shiyyar Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa maso Tsakiya, wanda ke neman durƙusar da kasuwanci.
Tinubu ya ba da umarnin gyara lantarki
A baya mun ruwaito cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umarci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen matsalar lantarki a Arewa.
Shugaban ya kuma bayyana rashin jin dadin yadda aka lalata manyan layukan wuta wanda ya jawo gagarumar matsala da koma bayan tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng