Abin da Gwamnoni da Sarakunan Arewa Suka Fadawa Tinubu, Sun Yi Fatali da Shirinsa
- Shugabanni a Arewacin Najeriya sun nuna damuwa kan sabon kudiri da ke gaban Majalisar Tarayya na haraji
- Gwamnoni da sarakunan gargajiya sun ki amincewa da kudirin, suka ce hakan ya saba muradun mutanen yankinsu
- Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar da Gwamna Inuwa Yahaya su suka jagoranci ganawar da aka yi domin samo mafita ga Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Gwamnonin Arewacin Najeriya da sarakunan gargajiya sun yi zama kan matsalolin da suka addabi yankin.
Shugabannin a Arewa sun yi fatali da kudirin karin haraji a kasar inda suka goyi bayan kirkirar ma'aikatar kiwon dabbobi.
Gwamnonin Arewa sun yabawa yaki da ta'addanci
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa bayan ganawar da Gwamna Inuwa Yahaya da Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar suka jagoranta, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin taron, gwamnonin da sarakunan gargajiya sun yabawa matakan da ake dauka wurin yaki da ta'addanci a yankin.
Sun nuna damuwa kan kudirin rarraba harajin inda suka ce zai kawo cikas ga muradun Arewacin kasar.
Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce ba su fada da duk wani tsari da zai kawo cigaba a kasar baki daya.
Shawara da gwamnonin Arewa suka ba Tinubu
Sai dai ya bukaci daidaito da adalci wurin aiwatar da duk wasu tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya a kasa.
Ya ce hakan zai tabbatar da samun daidaito ba tare da nuna wariyar ko cutar da wani yanki na kasar ba, cewar Daily Trust.
Sun yi kira ga Majalisar Tarayya da ta ki amincewa da duk wani tsari da zai sake jefa al'ummar Najeriya cikin wani hali.
Jigawa: Gwamnonin Arewa sun ba da gudunmawa
Kun ji cewa yayin da ake cigaba da jimamin rasa rayuka a jihar Jigawa, gwamnonin Arewacin Najeriya sun ba da tallafi mai tsoka.
Shugaban gwamnonin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa gwamnatin jihar da al'umma kan wannan iftila'i da ya afku.
Gwamna Inuwa ya ce domin ragewa waɗanda abin ya shafa radadi, kowane gwamna a yankin zai ba da gudunmawar N50m.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng