Gwamnonin Arewa Sun Farga, Sun Gane Dalilin da Talauci Ya Fi Ƙamari a Shiyyarsu
- Gwamnonin jihohin Arewa sun ce talauci ya fi ƙamari a shiyyar nan idan aka kwatanta da jihohin da ke Kudu
- Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ne ya bayyana haka a taronsu a Kaduna
- Ya bayyana cewa gwamnoni za su samar da shirin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya domin warware matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gwamnonin jihohin Arewa sun gano cewa talaucin da ake fama da shi a Najeriya ya fi kamari a shiyyar nan.
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ne ya sanar da damuwar da su ka shiga a taron da ke gudana a Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnonin sun kuma bayyana takaicin yadda ake fama da tsananin rashin hasken wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Arewa sun fadi dalilin kamarin talauci
Jaridar The Cable ta tattaro cewa gwamnonin Arewacin Najeriya sun ce talauci ya yi ƙamari a Arewa saboda rashin daidaiton tattalin arziki da Kudancin kasar nan.
Gwamnonin sun ce akwai bukatar su hada hannu da gwamnatin tarayya da hukumomi wajen gaggauta magance barazanar da shiyyar ke fuskanta.
Gwamnonin jihohin Arewa sun tattauna matsalarsu
Gwamnonin jihohin Arewa sun hallara a jihar Kaduna inda su ka gana da babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa.
Matsalolin da aka gano sun saka Arewa a gaba sun hada da yawan yara marasa zuwa makaranta, garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya da ta'addanci.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce waɗannan matsaloli ne su ka su taruwa a Kaduna domin nemo hanyoyin kawo karshen matsalolin.
Obi ya yi fargabar ƙaruwar talauci a Arewa
A baya mun ruwaito cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya ce ƙamarin rashin wuta a Arewacin Najeriya zai kara jefa jama'a a cikin talauci.
Ya ce haka zai iya faruwa ganin yadda rashin hasken wutar ke durkusawar da kasuwanci, musamman kasuwancin da ke tasowa da kuma dogara da wuta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng