Kwanaki 8 a Duhu: Yadda Rashin Wuta ke Durƙusar da Kasuwanci da Sana'o'i a Arewa

Kwanaki 8 a Duhu: Yadda Rashin Wuta ke Durƙusar da Kasuwanci da Sana'o'i a Arewa

  • An shafe kwanaki takwas babu wutar lantarki a mafi yawan jihohi a Arewacin Najeriya wanda har yau babu ranar kammala gyara
  • Rashin wuta ya jefa al'umma a wahalar rayuwa da karyewar tattali kasancewar lamarin ya jawo dakatar da harkokin yau da kullum
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku yadda sana'o'i suka fara durkushewa a Arewacin Najeriya sakamakon rashin wutar lantarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - A halin da ake ciki, Arewacin Najeriya ya shafe kwanaki takwas ba tare da samun wutar lantarki ba.

Lamarin ya jawo mutanen yankin na Arewa sun shiga cikin damuwa kasancewar harkokin kasuwanci sun tsaya.

Lantarki
Ana asara a Arewa saboda rashin lantarki. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta haɗa rahoto kan yadda rashin wuta ke kawo koma baya a kasuwancin Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ragargaji Tinubu, ya fadi yadda rashin wuta zai yi wa Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rashin wutar lantarki ya shafi Arewa

1. Kano

Masu sayar da abinci a bakin asibitin Aminu Kano sun bayyana cewa kullum a cikin asara suke saboda rashin wuta.

Yan kasuwar sun ce ba su da wuraren ajiye kayan abinci saboda kaucewar lalacewa.

Wannan zai jawo asara da rashin dukiya don haka ne aka ji wasu jagororin Arewa suna cewa a nemi wata mafita.

2. Gombe

A Gombe, wani mai sayar da kifi, Muhammad El-Kabeer ya bayyana cewa rashin wuta ya jefa su cikin asara sosai.

Muhammad El-Kabeer ya ce dole su rika tayar da inji domin samun wuta kuma haka yana sanya su kashe kudi sosai.

Wani mai harkar shinkafa ya bayyana cewa ayyuka sun tsaya saboda rashin wuta a wuraren sana'o'insu.

3. Kebbi

Wani mai sayar da kifi, Bashir Abdullahi ya ce ban da asara babu abin da suke tafkawa sakamakon rashin wuta.

Kara karanta wannan

Ana bakin kokari, TCN ya fadi lokacin dawowar hasken lantarki a Arewa

Bashir Abdullahi ya kara da cewa wasu bata gari sun sace karafuna a randar wuta da ke ba su lantarki.

4. Filato

Masu aikin katako a jihar Filato sun ce a yanzu haka mutane sun daina zuwa sayen kaya a wajensu.

A wasu wurare kamar unguwar Rogo bata gari sun shiga sun sace kayan a randar wutar lantarki.

5. Kaduna

Wata budurwa, Halima Mua'azu ta ce sana'ar mahaifiyarta ta sayar da zobo ta tsaya cak tun bayan dauke wuta.

Masu saida kifi sun gamu da asarar makudan kudi, wasu kuma dole ta sa sun gasa su domin gudun karyewar jarinsu,

6. Benue

Wata mata mai sayar da kifi, Mwuese Terkula ta ce idan lamarin ya cigaba a haka dole ta dakatar da sana'a saboda ba kudin da za ta rika saka mai a inji.

Tsadar man fetur na cigaba da barazana ga sana'o'i a Benue ta inda ake sayen lita a kan N1,200 zuwa 1,250.

Kara karanta wannan

Wutar Arewa: Kwankwaso ya kawo mafita ga gwamnonin jihohi

7. Bauchi

Wani mai sayar da kayan gwari ya bayyana cewa kasuwa ta ja baya kasancewar mutane sun daina saye su adana kaya a gidaje.

8. Adamawa

Wata mata mai sayar da kayan gwari, Hajiya Asma'u ta ce ta tafka asara sosai saboda rashin wuta.

9. Taraba

Wani mahauci a jihar Taraba, Yunusa Adamu ya ce yanzu haka kasuwa ta ja baya kuma ana tafka asara saboda rashin kayan sanyaya nama.

10. Nasarawa

Wata mata a jihar Nasarawa, Aisha Umar ta koka da cewa kasuwancinsu ya ja da baya kasancewar abubuwa sun tsaya cak.

Matsalar wuta a sauran jihohin Arewa

Haka zalika ake fama da matsalolin lantarki a jihohin Borno, Yobe, Kwara, Zamfara Katsina da sauran jihohin Arewa.

Har yanzu ba a samu tabbacin lokacin da za a dawo da lantarki a Arewacin Najeriya ba duk da cewa TCN ta ce ta dukufa da gyara.

Kwankwaso ya yi magana lantarki

Kara karanta wannan

Lalacewar wuta: Atiku ya dauki zafi kan lamarin, ya kawo hanyar dakile matsalar

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa Sanata Rabi'u Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda ake fama da matsalar lantarki a Arewa.

Sanata Rabi'u Kwankwaso ya ce akwai bukatar gwamnonin jihohi su samar da wuta a yankunansu domin kaucewa shiga irin yanayin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng