Peter Obi Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Yadda Rashin Wuta Zai Yi wa Arewa

Peter Obi Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Yadda Rashin Wuta Zai Yi wa Arewa

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan rashin gyara wutar Arewa
  • Peter Obi na taya yan Arewa bakin cikin duhu da su ke ciki na tsawon kwanaki takwas wanda ya jefa jama’a a cikin matsi
  • Ya bayyana cewa tsadar fetur ya kara dagula matsalar rashin wuta, domin jama’a ba za su iya saye domin samun sauki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya ce rashin wutar lantarki a Arewacin kasar nan babbar matsala ce.

Kara karanta wannan

Ana bakin kokari, TCN ya fadi lokacin dawowar hasken lantarki a Arewa

Ya ce matsalar ta kara ta’azzara saboda tsadar da litar fetur ta yi, wanda ke hana jama’a samun wuta ta hanyar tayar da injin janareto.

Peter
Peter Obi ya caccaki Tinubu kan rashin wuta a Arewa Hoto: Mr. Peter Obi/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Peter Obi ya bayyana haka ta ne ta sakon da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce rashin wuta ya jefa kasuwanci a Arewacin kasar nan cikin babbar matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi: "illar rashin wuta a Arewa"

Kafar Channels Television ta tattaro Peter Obi ya bayyana fargabar rashin wuta zai kara jefa jama’a a cikin talauci saboda kasuwanci na cikin wani hali.

Ya kara da cewa tsadar fetur da rashin wutar lantarkin za su durkusar da kasuwanci, musamman na ‘yan kasuwa masu tasowa a yankin Arewa.

An shawarci gwamnati kan gyara lantarki

Tsohon dan takarar shugaban kasar nan a jam’iyyar LP, Peter Obi ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gaggauta gyara wutar lantarki a Arewacin kasar nan.

Kara karanta wannan

'Ku kara hakuri': Gwamnati ta bayyana inda aka kwana game da gyaran wutar Arewa

Ya bayyana cewa gwamnati za ta iya sake fasalta wutar lantarki a kasar nan kamar yadda kasashe irinsu Egypt da ake samun wadatar wuta.

Arewa: TCN ya ce ana gyaran lantarki

A wani labarin, kun ji cewa kamfanin wutar na kasa (TCN) ya ce Injiniyoyinsa su na aiki tukuru domin dawo da hasken wutar lantarki jihohin da ke Arewa.

Manajan hulda da jama’a na kamfanin, Ndidi Mbah ne ya bayar da tabbacin, tare da musanta cewar babu ranar gyara hasken wutar lantarki Arewacin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.