Mafi Karancin Albashi: Gwamnan APC Ya Amince da N75,000, Ya Fadi Lokacin Biya

Mafi Karancin Albashi: Gwamnan APC Ya Amince da N75,000, Ya Fadi Lokacin Biya

  • Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin da zai biya ma'aikata a jihar
  • Nwifuru ya amince da N75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar da ke yankin Kudu maso Gabas
  • Gwamnan ya kuma sanar da cewa za a fara aiwatar da albashin ne daga ranar Litinin, 28 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayyana mafi ƙarancin albashin da zai biya ma'aikata.

Gwamna Francis Nwifuru ya amince da biyan N75,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamnan Ebonyi ya amince da mafi karancin albashi
Gwamna Francis Nwifuru ya amince da mafi karancin albashin N75,000 Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Monday Uzor, ya fitar a birnin Abakaliki ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamna ya amince da biyan N70,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Ebonyi ya amince da N75,000

Gwamna Nwifuru ya ce za a fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ne a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoban 2024, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Gwamnan ya bayyana cewa, matakin ya biyo bayan nazari sosai kan halin da tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki musamman yadda ya shafi ma’aikata.

A cewar gwamnan, ma’aikacin da ke a mataki na biyu zai samu cikakken mafi ƙarancin albashi na 75,000 yayin da ma'aikata daga mataki na uku zuwa sama za su samu ƙarin N40,000.

Gwamna Nwifuru ya kuma sanar da naɗin manyan manajojin da za su jagoranci manyan masana’antu guda biyu a jihar.

Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamna ya fara hasashen biyan N1m ga ma'aikata

Gwamna Soludo zai biya sabon albashin N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar nan take.

Gwamna Soludo ya bayyana cewa ma’aikaci mafi karancin albashi a jihar Anambra zai samu abin da bai gaza N70,000 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng