An Bi Gida Gida, An Kashe Mutane a Rikicin Manoma da Makiyaya

An Bi Gida Gida, An Kashe Mutane a Rikicin Manoma da Makiyaya

  • Rikici ya sake ballewa tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa, inda rayukan jama'a su ka salwanta
  • An yi zargin wasu da ake zargin makiyaya ne sun bi gidajen mazauna Kukta da ke Waltandi da ke karamar Song
  • A wannan harin, an salwantar da rayukan mutane biyar, kuma yan sanda sun tabbatar da cewa yanzu haka ana bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Adamawa - An shiga fargaba bayan kisan mutane da dama yayin da rikici ya balle tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa, inda jama'a da dama su ka rasa rayukansu.

Rikicin ya afku ne a yankin Kukta da ke Waltandi da ke karamar Song da ke Adamawa.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya bindige fitaccen mawaki a Najeriya, rundunar ta dauki mataki

Fintiri
Mutane 5 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Adamawa Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an shafe kwanaki ana rikicin da ya jawo asarar rayukan mutane da dama a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe manoma a Adamawa

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa wasu da ake zargi makiyaya ne sun kai hare-hare gidajen jama’a tare da kashe mutane biyar a mummunan harin.

Mazauna garin sun bayyana cewa an kai harin ne a matsayin ramuwar gayya, duk da dai babu tabbacin ikirarin harin na ramuwar gayya ne.

An dauki mataki kan rikicin Adamawa

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kai dauki mataki wajen dawo da zaman lafiya yankin da rikici ya balle.

Kwamishinan yan sandan Adamawa, Dankombo Morris ya bayar da umarnin a zurfafa bincike domin gano abin da ya jawo rikicin.

Adamawa: Yan sanda sun kama yan daba

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke Bobrisky da tsakar dare yana shirin guduwa daga Najeriya

A wani labarin kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da damke wasu yan daba da ake zargi da yunkurin kashe wani jami'in rundunar bayan sun dauke shi a adaidaita sahu.

Jami’in hulda da yan sanda na rundunar yan sandan Adamawa, SP Sulaiman Yahaya Ngurore ya ce za a gurfanar da yan daban a gaban kotu domin a hukunta su daidai da abin da su ka aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.