Ministan da Tinubu Ya Kora Ya Gana da Tsohon Gwamnan Kano, an Samu Bayanai

Ministan da Tinubu Ya Kora Ya Gana da Tsohon Gwamnan Kano, an Samu Bayanai

  • Malam Ibrahim Shekarau ya gana da karamin ministan gidaje da raya birane da shugaba Bola Tinubu ya kora, Abdullahi Tijjani Gwarzo
  • Wata sanarwa da Abdullahi Gwarzo ya fitar ta nuna cewa tsohon gwamnan Kano ya gana da tsohon ministan domin taya shi murna
  • A ziyarar da ta jawo mutane suka yi martani game da sallamar Gwarzo, akwai Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar yankin Kano ta Kudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Abdullahi Tijjani Gwarzo, tsohon karamin ministan gidaje da raya birane ya gana da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tare da Malam Shekarau, tshon ministan ya kuma gana da Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wata magana, ya roki ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa Tinubu addu'a

Tsohon minista ya gana da tsohon gwamnan Kano
Abdullahi Gwarzo: Tsohon ministan gidaje ya gana da tsohon gwamnan Kano. Hoto: @ATMgwarzo
Asali: Twitter

Abdullahi Gwarzo ya sanar da ganawarsa da tsohon gwamnan tare da Sanata Sumaila a shafinsa na X a daren Lahadi, 27 ga Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwarzo ya gana da tsohon gwamnan Kano

Tsohon ministan ya sanar da cewa ya gana da manyan 'yan siyasar biyu ne a gidansa, inda ya ce:

"Na yi farin cikin karbar bakuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu a gidana a yau."

Abdullahi Gwarzo, ya yi nuni da cewa ziyarar Malam Shekaru da Kawu Sulaiman na da alaka ne da kujerar ministan da shugaba Bola Tinubu ya sauke shi.

"Sun zo ne domin su taya ni murna da addu’o’in na samun nasarar kammala wa'adin da Allah ya kayyade mun a matsayin minista."

- A cewar tsohon ministan.

Mutane sun yi wa Gwarzo fatan alheri

Kara karanta wannan

Tinubu, Ganduje sun yi kicibis da Atiku da manyan yan adawarsa a siyasa, bayanai sun fito

Masu bibiyar shafin tsohon ministan, sun yi masa fatan alkairi tare da addu'ar Allah ya kawo wani rabon a nan gaba.

@AliyuubaleA:

"Allah ya sa hakan shi ne mafi alkairi a gare ka sir."

@Yasseer_din_mum:

"Masha Allahu, siyasa ba da gaba ba."

@Alameen_Zarewa ya ce:

"Allah ya dawwamar da farin ciki a fuskarka mai gida. Ko da mulki ko babu sai ka rayu cikin walwala da jin daɗi tunda kariƙe Allah, ATM Allah ya ƙara lafiya."

Tsohon minista ya aika sako ga Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya yi martani bayan shugaba Bola Tinubu ya raba shi da mukaminsa.

Awani da tsige shi daga kan kujerar minista, Gwarzo ya nuna godiyarsa kan damar da Tinubu ya ba shi domin ba da irin ta shi gudunmawar wajen kawo ci gaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.