Rigimar Saurata Ta Barke, an Gargadi Gwamna a Arewa kan Tabbatar da Sabon Sarki

Rigimar Saurata Ta Barke, an Gargadi Gwamna a Arewa kan Tabbatar da Sabon Sarki

  • An samu rigima kan nadin sarauta a jihar Kwara inda al'umma ke ganin an yi ba daidai ba wurin nadin wanda ba jinin sarauta ba
  • Mazauna yankin Oro a jihar Kwara sun bukaci Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya dakatar da tabbatar da nadin sarautar
  • Hakan ya biyo bayan mika sandar sarauta ga Oba Joel Olaniyi Oyatoye a matsayin Oloro na masarautar Oro a yau Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Nadin sarauta na neman dawowa babbar rigima a jihar Kwara bayan Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya nada sabon Sarki.

An bukaci gwamnan da ya dakatar da tabbatar da Oba Joel Olaniyi Oyatoye a matsayin Oloro na masarautar Oro.

Kara karanta wannan

Kusa a PDP ya soki Tinubu kan kyale Mawatalle a mukaminsa, ya fadi illar haka

An ba gwamna shawara kan nadin basarake ba bisa ka'ida ba
Mazauna masarautar Oro sun bukaci Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya dakatar da tabbatar da basarake. Hoto: AbdulRazak AbdulRahman.
Asali: Twitter

Gwamna ya nada basarake da ya jawo cece-kuce

Tribune ta ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya mika sandar sarauta Oba Joel Olaniyi Oyatoye a yau Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna AbdulRahman ya samu wakilcin mataimakinsa, Kayode Alabi yayin bikin da aka gudanar a birnin Ilorin a yau Lahadi.

Sai dai mazauna yankin Oro sun koka inda suka ce Oba Oyatoye ba jinin sarauta ba ne dole a bi tsarin da ya dace.

Zargin da ake yi kan badakalar nadin sarauta

Sun zargi kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar, Hon. Abdullahi Abubakar Bata da kakabawa al'umma Sarkin da kuma daukar nauyinsa.

Har ila yau, sun tabbatar da cewa rigimar masarautar na gaban kotun majistare da ke Omu Aran wanda za a yi hukunci a ranar 4 ga watan Nuwambar 2024, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zama na farko a Arewa da ya amince da N80,000 a matsayin sabon Albashi

Daga bisani sun bukaci gwamnan da ya mutunta dokar kasa duba da yadda lamarin ke gaban kotu a matsayinsa na Gwamna.

Gwamnan Kwara zai biya mafi ƙarancin albashi

Kun ji cewa ma'aikatan gwamnati a jihar Kwara za su fara cin moriyar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 daga watan Oktoba, 2024.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya umarci a fara biyan sabon al.bashin nan take bayan ganawa da ƴan kwadago da kamfanoni.

Kwamishinar kuɗi ta jihar Kwara, Dr. Hauwa Nuru ta ce wannan mataki ya kara nuna yadda gwamna ya himmatu wajen inganta walwalar ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.