‘Ba a Son Ranmu ba ne': Mabarata ga Ministan Tinubu da Yake Shirin Fatattakarsu

‘Ba a Son Ranmu ba ne': Mabarata ga Ministan Tinubu da Yake Shirin Fatattakarsu

  • Kwanaki biyu bayan Nyesom Wike ya umarci korar mabarata, wasu masu bara sun mayar masa da martani
  • Mafi yawan mabaratan sun koka kan yadda ake kokarin fatattakarsu ba tare da duba halin da za su shiga ba
  • Hakan ya biyo bayan umarnin Wike kan zargin wasu daga ciki da miyagun ayyuka a birnin inda ya ce ba zai lamunta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Bayan umarnin kame da kuma korar mabarata a Abuja, mabarata sun bayyana damuwa kan haka.

Mabaratan sun koka kan shirin fatattakarsu a Abuja ba tare da samar musu da wata hanya domin samun na kashewa ba.

Mabarata sun mayar da martani ga Wike kan shirin korarsu
Mabarata sun caccaki Nyesom Wike kan shirin fatattakarsu a birnin Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Twitter

Wike ya shirya korar mabarata a Abuja

Kara karanta wannan

Yan sanda sun fadi abin da ya jawo gini ya rufta kan mutane masu yawa a Abuja

Wakilin Punch ya tambayi wani mabaraci kan lamarin inda ya ce bai san mene suka yi ba da za a dauki wannan mataki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan umarnin da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da a fara kamen mabarata daga gobe Litinin 28 ga watan Oktoban 2024.

Wike ya zargi wasu daga cikin mabaratan da cika birnin inda miyagu ke fakewa a cikinsu domin aiwatar da munanan ayyuka, cewar Channels TV.

Wani mabaraci, Ali Bappah ya ce bai san da umarnin ba inda ya yi mamaki idan akwai shirin samar musu da wata hanya.

Ya ce kwata-kwata ba a son ransa yake fita yin bara ba domin neman abinci inda ya koka kan yadda ake nuna musu wariya a Abuja.

"Wannan hali dana tsinci kai na ba abu ne da nake so ba a rayuwa ta, babu wanda ya fi karfin haka ta faru da shi, wasu gudunmu suke yi idan sun ganmu."

Kara karanta wannan

2027: Manyan yan siyasar Arewa sun fara hada kai, suna ganawa kan tumbuke Tinubu

"Ko a motar kasuwa babu wanda yake son hada wurin zama da mu, saboda wasu suna tsammanin yin mu'amala da mu zai mayar da su makafi."

- Ali Bappah

Wani mabaraci ya magantu kan matakin Wike

Har ila yau, wani mabaraci, Safiyanu Bako ya ce bai san da dokar ba amma zai bar birnin Abuja domin komawa jiharsa ta Kebbi ya cigaba da kasuwanci.

Bako ya ce kama mabarata kwata-kwata ba ita ce mafita ba musamman a wannan hali na matsin tattalain arziki da ake ciki.

Wike ya sake rokon yan Najeriya

Kun ji cewa Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu addu'a.

Wike ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kinkimo aiki mai girma wanda ke buƙatar addu'a domin cimma nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.