Mahaifiyar Sarki Mai Daraja Ta 1 a Najeriya Ta Rigamu Gidan Gaskiya, an Samu Bayanai
- Allah ya yiwa mahaifiyar sarkin masarautar Owu da ke Abeokuta, jihar Ogun, Oba (Farfesa) Saka Adelola Matemilola rasuwa
- An rahoto cewa Alhaja Alirat Ayinke Matemilola, mahaifiyar sarkin ta rasu tana da shekaru 81 a ranar Lahadi, 27 ga Oktoba
- Dan marigayiyar, Mista Soliu Matemilola ne ya sanar da rasuwar Alhaja Alirat inda aka rahoto lokacin da za a yi jana'izarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - Sarkin masarautar Owu da ke Abeokuta, jihar Ogun, Oba (Farfesa) Saka Adelola Matemilola ya yi babban rashi na mahaifiyarsa.
Masarautar Owu ita ce kasar haihuwa ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Mahaifiyar Sarkin Owu, Alirat ta rasu
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Alhaja Alirat Ayinke Matemilola (Née Bolaji), mahaifiyar sarkin ta rasu tana da shekaru 81.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce mahaifiyar Sarki Saka Adelola ta rasu ne a safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2024.
An ce marigayiya Alhaja Alirat Ayinke ta rasu ta bar ‘ya’ya bakwai; maza biyar da mata biyu.
'Ya'yan da ta bari sun hada da Oba Matemilola; Alhaja Fatimah Adéyemí; Musa Matemilola and Hafeez Matemilola – wadanda dukkaninsu injiniyoyi ne.
An sanya lokacin binne mahaifiyar sarki
Misis Mujidat Arogundade; Dakta Saheed Matemilola da Mista Soliu Matemilola.
Da yake tabbatar da mutuwar mahaifiyar sarki, ɗan marigayiyar, Soliu ya rubuta cewa:
“Na rasa mahaifiyata a safiyar yau da misalin karfe 7:30 na safe. Ta rasu a hannun Sarki Olowu a Abeokuta."
Rahoton ya bayyana cewa za a yi jana’izar marigayiya Alhaja Matemilola a makabartar Abari da ke isalẹ Ekọ Lagos Island da karfe 2 na rana.
Dada: Mahaifiyar 'Yar'adua ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa mahaifiyar Hajiya Dada Ƴar'adua, mahaifiyar tsohon shugaban kasar Najeriya, Umar Musa Yar'adua ta kwanta dama.
Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Dada ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya yau Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024, tana da shekaru 102 a duniya.
Asali: Legit.ng