Matan da Za Su Shiga Gwamnatin Bola Tinubu bayan Sauyi a Majalisar FEC

Matan da Za Su Shiga Gwamnatin Bola Tinubu bayan Sauyi a Majalisar FEC

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauyi a majalisar zartarwa, ya kori wasu kuma ya kara wasu ministocin gwamnatinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Fadar shugaban kasa ta sanar da Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin minista da aka yi canji a majalisar zartarwa da ake kira FEC.

Mun yi kokarin tattaro bayanai game da matan da aka zaba domin su zama ministoci.

Ministoci
Sababbin ministocin Bola Tinubu Hoto: Abdalla Uba Adamu/@joduwole/allafrica.com
Asali: UGC

Matan da za su zama ministoci

1. Suwaiba Said Ahmad

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Suwaiba Said Ahmad ta na cikin wadanda za su iya shiga majalisar FEC, ta kware a harkar malanta da kwatowa mata hakkokinsu.

Malama ce a jami’ar Bayero da ke Kano da ta rike mukamai dabam-dabam. Bayan nan ta yi aikin bincike da manyan kungiyoyin duniya.

Kara karanta wannan

Raba kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai ya hango makomar Najeriya

A shafinsa na Facebook, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana cewa da farko ta yi sha’awar zama likita ne amma ta kasance malama.

Idan an tantance ta a majalisar dattawa, za ta zama karamar minister ilmi ta na da shekaru 43 da haihuwa, kusan ‘yar auta a cikin mata.

2. Bianca Odumegwu-Ojukwu

Ita Bianca Odumegwu-Ojukwu jakada ce kuma za a iya kiranta lauya sannan ‘yan kasuwa bayan kasancewarta sarauniyar kyau a Najeriya.

A shekarar 2011, shugaba Goodluck Jonathan ya nada Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin 'yan ci-rani.

Kafin ta zama jakadar Najeriya a kasashen Ghana da Sifen kafin zama wakiliyar Najeriya a kungiyar bude ido majalisar dinkin duniya.

Bola Tinubu ya na so mai dakin ta Chukuemeka Odumegwu-Ojukwu ta zama karamar ministar harkokin waje karkashin Yusuf Tuggar.

3. Dr. Jumoke Oduwole

Dr. Jumoke Oduwole za ta canji tsohuwar ministar masana’antu, kasuwanci da zuba hannun jari kamar yadda sanarwa ta gabata.

Kara karanta wannan

Jerin ministocin da Tinubu ya kora daga aiki da jihohin da suka fito a Najeriya

Jaridar Nairametrics ta ce kafin zabenta, ta na cikin masu taimakawa mataimakin shugaban kasa kuma ita ce hadima a bangaren PEBEC.

Jumoke Oduwole ta fara karatun ilmin shari’a ne a jami’ar Legas. Daga baya sai ta je jami’o’in Cambridge, Stanford da Oxford a waje.

Lokacin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi kokarin saukaka kasuwanci, magajiyar Doris Nkiruka Uzoka-Anite ce ta rike sakatare.

INEC ta yi shugabanni 4 a watanni 3

Ana da labarin yadda Goodluck Jonathan ya nada Farfesa Attahiru Jega a 2010 wanda ya yi wa’adi sau biyu sai ya sauka a Yulin 2015.

Lokacin da Attahiru Jega zai bar ofis, sai ya zabi Ahmad Wali ya zama shugaban rikon kwarya daga nan aka kawo Amina Zakari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng