Buhari ya saba dokar Hukumar NAPTIP wajen nada Imaan Sulaiman-Ibrahim
- Imaan Sulaiman-Ibrahim ba ta cika sharudan da za ta rike Hukumar NAPTIP ba
- Bincike ya tabbatar da cewa Mrs Sulaiman-Ibrahim ba Darekta ba ce a Gwamnati
- Shugaba Muhammadu Buhari ya saba dokar kasa wajen ba ta wannan mukamin
Wajen nada Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin sabuwar shugabar hukumar NAPTIP, shugaba Muhammadu Buhari ya saba dokar da ta kafa hukumar.
Premium Times ta gudanar da wani bincike na musamman da ya nuna yadda shugaban Najeriya ya yi fatali da sashe na 8(1) na dokar NAPTIP ta 2015.
Abin da dokar hukumar NAPTIP ta 2015 ta ce shi ne dole Darekta Janar ya zama babban ma’aikacin gwamnati ko kuma ya kasance jami’in tsaro.
Sai ma’aikacin da ya kai mukamin akalla Darekta a gwamnati ko wani makamancin haka a gidan ‘yan sanda ko wani aikin khaki ne zai rike hukumar kasar.
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa maso gabas sun yarda da shawarar Zulum
Jaridar ta ce binciken da ta yi, ya nuna mata cewa ko ta ina Misis Sulaiman-Ibrahim ba ta cika wadannan sharuda da gwamnatin tarayya ta gindaya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sashen dokar da ta bada damar a kafa shugaba ko Darekta Janar wanda zai jagoranci hukumar NAPTIP, ya ce Minista ne zai bada shawarar wanda za a nada.
Sulaiman-Ibrahim, ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa wanda babu ta inda ta cancanci ta rike wannan kujera da shugaban kasar ya ba ta, idan aka bi dokar aiki.
Wannan Baiwar Allah ta na kasuwanci ne da Mary Kay products, ba ta rike da kujerar Darekta a aikin gwamnati, bayan haka, ba jami’ar tsaro ba ce a Najeriya.
KU KARANTA: Jagororin APC sun tado maganar yi wa tsarin mulki garambawul
Haka zalika, Okah-Donli wanda ta ke rike da hukumar kafin yanzu, ba ta cika sharudan zama Darekta Janar ba, amma aka ba ta wannan mukami a shekarar 2017.
Dazu nan ku ka ji cewa hukumar PSC ta jefi IGP da NPF da laifin cusa sababbin ‘Yan Sanda 900 a aiki ta bayan fage, ba tare da sun nemi aikin, ko an tantance su ba.
Fiye da 9% na wadanda aka ba aikin ‘yan Sanda a bana ba su cika sharuda ba, sai dai hukumar PSC ta dauke su aiki a haka saboda an riga an soma basu masu horo.
PSC ta ce ta bankado yadda aka saba doka wajen daukar aikin, amma ta sake bin lamarin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng