‘Dan Majalisa Ya Bukaci a Binciki ‘Son Kai’ da Aka Yi Wajen Daukar Aiki a Hukumomi 3

‘Dan Majalisa Ya Bukaci a Binciki ‘Son Kai’ da Aka Yi Wajen Daukar Aiki a Hukumomi 3

  • Majalisar wakilan tarayya ta na tuhumar wasu ma’aikatun gwamnati da saba doka wajen daukar ma’aikata
  • ‘Yan majalisa sun ce ya kamata a binciki hukumomin FIRS, CAC da kuma NDIC kan zargin yin ba daidai ba
  • An kafa kwamiti da zai yi wannan aiki kuma ya gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin makonni hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ce za ta binciki zargin saba doka wajen daukar aiki a wasu hukumomin gwamnatin Najeriya.

An dade ana zargin cewa ana rashin gaskiya wajen rabon aiki musamman a ma’aikatun gwamnati, ba a bin dokoki da tsarin aiki.

Majalisa
'Yan majalisa za su binciki daukar aikin gwamnati Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Za a binciki daukar aikin hukumomin gwamnati

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X da ya fi shahara da Twitter Ali Isa ya tabbatar da cewa ya bijiro da maganar a majalisar.

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan majalisar ya ce ya gabatar da kudiri domin a binciki hukumar FIRS mai alhakin tattara haraji da kuma CAC mai rajistar kamfanoni.

Binciken majalisa zai shafi hukumar NDIC

Haka zalika ‘dan majalisar na Gombe ya nemi a yi bincike game da yadda aka dauki ma’aikata a hukumar NDIC mai ba bankuna kariya.

Daga cikin zargin da yake yi shi ne ana son kai wajen rabon aikin; ba a yin adalci tsakanin al’umma, sai dai a yi amfani da doguwar kafa.

Yaushe majalisa za ta gama binciken?

Daily Trust ta ce ana zargin hukumomin da facaka da kudin gwamnatin tarayya don haka kwamiti za a yi bincike a cikin makonni hudu.

Idan zargin sun tabbata, shugabannin wadannan manyan hukumomi za su amsa tambaya game da cin amana da watsi da dokar daidaito.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

‘Dan majalisar ya ce idan za a dauki aiki, doka ta bukaci a yi gaskiya kuma dole a tafi da kowane bangare ba tare da an nuna wariya ba.

The Cable ta ce shugaban masu tsawarta da marasa rinjayen ya dauko wannan yunkuri ne a zaman da aka yi na ranar alhamis.

Idan ana son kai da rashin gaskiya wajen daukar aiki a ma’aikatun nan, Isa Ali ya ce hakan ba zai bari su iya yin aikinsuNDIC da kyau ba.

'Dan majalisar da ke sukar Tinubu

Majalisar tarayya ta 10 ba ta dade da kafuwa ba sai aka ji labari Ali Ndume ya na kokawa da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Sanatan Bornon ya fito baro-baro ya fadawa shugaban kasa cewa an katange shi cikin fadar Aso Villa kuma ya soki tsare-tsarensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng