Mafi Karancin Albashi: Gwamna Ya Amince da Biyan N70,000

Mafi Karancin Albashi: Gwamna Ya Amince da Biyan N70,000

  • Gwamnatin jihar Anambra ta amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma'aikatan jihar
  • Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya kuma sanar da fara biyan ƴan fansho N10,000 har zuwa lokacin da za a sake duba albashinsu
  • Gwamna Soludo ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin ne bayan wani taro tare da ƙungiyoyin ƙwadago na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya sanar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikata a jihar nan take.

Gwamna Soludo ya bayyana cewa ma’aikaci mafi karancin albashi a jihar Anambra zai samu abin da bai gaza N70,000 ba, duk da cewa zai iya zama tsakanin N78,000 zuwa N84,000.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamna ya fara hasashen biyan N1m ga ma'aikata

Gwamnan Anambra ya amince da mafi karancin albashi
Gwamna Soludo ya amince da biyan mafi karancin albashi Hoto: Prof. Charles Soludo
Asali: Twitter

Gwamna Soludo ya amince da biyan N70,000

An sanar da hakan ne bayan wani taro tsakanin shugabannin kwadago daban-daban na jihar da gwamnatin jihar wanda aka gudanar a yammacin ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Soludo ya kuma amince da bayar da tsabar kudi N10,000 duk wata ga duk masu karbar fansho a jihar, har zuwa lokacin da za a sake duba albashin fansho.

Mambobin ƙungiyoyin ƙwadagon sun samu jagorancin shugaban ƙungiyar NLC, Humphrey Nwafor da shugaban ƙungiyar TUC Chris Ogbonna da Shugaban ƙungiyar JNC, Edith Onwuka.

Kungiyoyin da shugabanninsu suka wakilta sun haɗa da NUJ, JUSUN, NULGE, NUT, NUP, da dai sauransu.

A ɓangaren tawagar gwamnati akwai sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma'aikata, babban mai binciken kudi na jiha, kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare da dai sauransu.

Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahu, ya bayyana sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata

Gwamnan Anambra ya ƙirƙiro sabuwar doka

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya ce ba wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Gwamna Soludo ya bayyana haka ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2024 a gidan gwamnati da ke Awka, bayan ya sanya hannu a kan kudirin dokar kananan hukumomin jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng