'Zan Taya Shi Fada': Korarriyar Minista Ta Fadi Matsayarta game da Tinubu bayan Ya Kore Ta

'Zan Taya Shi Fada': Korarriyar Minista Ta Fadi Matsayarta game da Tinubu bayan Ya Kore Ta

  • Korarriyar Minista a gwamnatin Bola Tinubu ta nuna goyon bayanta wurin taya shugaban inganta Najeriya
  • Uju Kennedy-Ohanenye ta ce Tinubu yana da tsare-tsare kuma ya himmatu wurin inganta Najeriya inda ta ce za ta kasance tare da shi
  • Hakan ya biyo bayan sallamar wasu Ministoci guda biyar inda ta kasance daga cikinsu a ranar 24 ga watan Oktoban 2024.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohuwar Ministar mata da aka kora, Uju Kennedy-Ohanenye ta sha alwashin tafiya tare da Bola Tinubu.

Kennedy-Ohanenye ta ce za ta cigaba da marawa Tinubu baya har zuwa karshe domin inganta Najeriya.

Tsohuwar Ministar mata ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu
Ministar mata da aka kora ta ce za ta kasance tare da Tinubu game da tsare-tsarensa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Uju Kennedy-Ohanenye.
Asali: Facebook

Tsohuwar Minista ta yabawa tsarin mulkin Tinubu

Kara karanta wannan

"Haka ya shiga ofis babu manufa:" Obasanjo ya zargi gwamnatin Tinubu da aiki da ka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohuwar Ministar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Asabar 26 ga watan Oktoban 2024 a shafinta na X.

Uju Kennedy ta ce ta aminta da tsare-tsaren shugaban kasa, Bola Tinubu inda ta roki yan Najeriya ka da su cire tsammani domin yana kan hanyar kawo sauyi a kasar.

Ta ce wannan bai wuce jarrawabawa ba wanda ko wane dan Adam mai imani ba zai tsallake ba a rayuwarsa kuma bai iya yin komai ba.

Uju Kennedy-Ohanenye ta nuna goyon baya ga Tinubu

"Bola Tinubu ya himmatu wurin inganta Najeriya, kuma ni, Uju Kennedy zan taya shi fafatawa har kashen fadan saboda irin shirinsa game da ƙasar"
"Wannan hali da ake ciki jarrawabawa ce da babu mai iya hanawa ko yin wani abu a kai, ya kamata mu yi fatan alheri ka da mu cire tsammani."

Kara karanta wannan

Dalilin Bola Tinubu na korar ministoci 5 ya bayyana, an faɗi asalin abin da ya faru

- Uju Kennedy-Ohanenye

Korarriyar Minista ta godewa Bola Tinubu

Mun baku labarin cewa tsohuwar Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi martani bayan sallamarta da Bola Tinubu ya yi a makon da ya wuce.

Uju Kennedy ta mika sakon godiya ga shugaban kasar da kuma mai dakinsa, Remi Tinubu kan irin goyon baya da suka bata yayin da take ofis.

Hakan ya biyo bayan sallamar Uju Kennedy da wasu Ministoci guda hudu a ranar 24 ga watan Oktoban 2024 bayan korafe-korafen yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.