Tsautsayi Ne: Malamin Sakandare Ya Yi Ajalin Dalibinsa Ta Hanyar Tsula Masa Bulala

Tsautsayi Ne: Malamin Sakandare Ya Yi Ajalin Dalibinsa Ta Hanyar Tsula Masa Bulala

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar wani dalibi da aka tsulale da bulala a makarantar sakandare
  • Rahoto ya bayyana yadda malamin makarantar sakandare ya kai ga yin ajalin dalibinsa bisa umarnin shugaban makaranta
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan lamari ba a makarantu a Najeriya, hakan ya sha aukuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Ogun - Wani malamin sakandare a makarantar Obada Idi-Emi da ke Imeko Afon a jihar Ogun ya yi ajalin dalibinsa mai suna Ariyo bayan tsulale shi da bulala har sau 162.

An ruwaito cewa, malamin ya dauki wannan mataki na zane dalibin ne bayan ya fasa kwandon shara a makarantar.

Kamar yadda wani dan fafutuka, Adetoun ya yada a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a, yanzu dai dalibin ya kwanta dama, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yadda 'yan ta'adda ke samun bindigogi da harsasan gwamnati,' sojoji sun yi bayani

Malami ya kashe dalibinsa a Legas
Labarin mutuwar dalibi a hannun malaminsa a Legas | Hoto: Nurphotos
Asali: Getty Images

Abin da ya hada Ariyo da malaminsa

A cewar Adetoun, malamin ya kawo kwandon shara ne ajinsu Ariyo, inda ya yi gargadin kada a fasa kwandon, lamarin da ya kai ga Ariyo ya saba maganar malamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa, cikin wasa Ariyo ya cewa malamin an sayi kwandon ne da kudin dalibai, martanin da bai yiwa malamin dadi ba.

An kuma bayyana cewa, tuni malamin ya kai maganar gaban shugaban makaranta, inda shugaban ya ce tabbas ya kamata a hukunta Ariyo kan wannan batu.

Laifin waye; shugaban makaranta ko malami?

Bisa umarnin shugaban makarantar ne malamin ya tsulawa Ariyo bulala har 162, wanda ana cikin haka ne ya fadi, bai farfado ba.

Adetoun ya kara da cewa, ganganci da jinkirin da malaman makarantar suka yi ne ya kai ga mutuwar dalibin ba tare da gaggauta daukar mataki ba.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin sa a daure iyaye kan rashin tura yara makaranta

Da take tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola ta ce, dalibin ya rasu ne a asibitin tarayya da ke Abeokuta.

Wani labarin na mutuwar dalibi a Legas

A wani labarin, ana zaman dar-dar a makarantar sakandare ta Araromi Ilogbo da ke Oko Afo, jihar Legas, bayan mutuwar wani dalibi, David Babadipo, wanda ake zargin dukan da wani malami ya yi masa ne ya yi ajalinsa.

Wasu bidiyoyi da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno dalibai cikin tashin hankali, suna ikirarin cewa wani malami mai suka Oluwale ya yi wa David duka har sai da ya bar duniya a ranar Alhamis.

Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya haddasa zanga-zanga a tsakanin daliban makarantar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.