Malamin Islamiyyan da ya yi wa Dalibi dukan da ya yi doguwar suma, ya shiga hannun ‘Yan Sanda

Malamin Islamiyyan da ya yi wa Dalibi dukan da ya yi doguwar suma, ya shiga hannun ‘Yan Sanda

- Wani Malami ya lakadawa Dalibinsa duka har ya shiga gargara a jihar Kwara

- ‘Yan Sanda sun damke wannan malami yayin da dalibin yake kwance a asibiti

- Za a gurfanar da Malamin Islamiyar da zarar ma’aikatan shari’a sun dawo aiki

Wata Lauya mai kare hakkin Bil Adama, Aishat Temin, ta yi Allah-wadai da danyen aikin wani malami da ya lakada wa dalibinsa mugun duka a jihar Kwara.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan malami mai suna Moshood Alabi ya jibgi dalibinsa ne har sai da ya yi doguwar suma saboda zargin ya saci kudi a asusu.

Tuni jami’an ‘yan sandan jihar Kwara su ka cafke wannan malami da ke koyar wa a makarantar Kur’ani.

Kamar yadda mu ka samu labari, bayan malamin ya zane yaron, sai ya umarci wasu dalibai uku su yi masa bulala goma-goma, a sanadiyyar ukubar ne ya sume.

KU KARANTA: Tarihin Shugaban farko da ya rike Jami’ar Bayero ta Kano da ya rasu

Da ta ke magana a gidan rediyon Diamond FM 88.7 a ranar Lahadi, Aishat Temin, ta ce babu inda doka ta ba malamin damar ya yi wa dalibinsa wannan mugun duka.

Haka zalika wannan Lauya ta ce doka ba ta halatta wa malamin makarantar addinin ba wasu iznin zane dalibin har ta kai ga ya suma saboda tsananin azaba ba.

“Malamin bai da damar zane yara a Islamiya. Idan yaron ya aikata wani laifi, za a iya yi masa karamin horo, bai da ikon da zai yi masa duka har ya ji masa ciwo.”

“Kuma bai da hurumin da zai umarci wasu dalibai su yi wa abokin karatunsu duka.” Inji Lauyar.

Malamin Islamiyyan da ya yi wa Dalibi dukan da ya yi doguwar suma, ya shiga hannun ‘Yan Sanda
Wata Makarantar allo a jihar Ribas
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram sun kashe mutane bayan sun kai sababbin hare-hare

Kakakin ‘yan sanda na jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya bayyana cewa jami’an tsaron da ke Oloje sun kama wannan malami, Moshood Alabi, bayan an kai masu kara.

Tun da malamin ya ji hukumar kare hakkin Bil Adama a Najeriya ta na nemansa, ya fara wasan buya da jami’an tsaro, a karshe dubunsa ta cika a karshen makon nan.

Yaron da aka yi wa wannan mugun duka ya na asibiti a garin Ilorin. Okasanmi ya ce ana binciken malamin, kuma za a kai shi kotu idan an janye yajin-aikin da ake yi.

Kwanakin baya an ji labarin abin kunya bayan an yi ram da wani Malamin makarantar allo da ya ke tara wa da kananan almajirai, wannan ya faru ne a jihar Sokoto.

Wannan ja'iri mai suna Malam Maude ya amsa laifinsa, amma ya ce yara uku rak ya taba yi wa fyade, amma an samu karin almajiran da su ka ce ya yi lalata da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel