Mafi Karancin Albashi: Gwamna Ya Fara Hasashen Biyan N1m ga Ma'aikata

Mafi Karancin Albashi: Gwamna Ya Fara Hasashen Biyan N1m ga Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya amince zai biya mafi ƙarancin albashin N80,000 ga ma'aikata
  • Gwamnan ya bayyana cewa nasarorin da jihar ta samu a ɓangaren noma, nam gaba za a iya biyan N1m a matsayin mafi ƙarancin albashi
  • Gwamna Bago ya nuna cewa za a fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashin ne daga watan Nuwamban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago ya bayyana mafi ƙarancin albashin da yake yunƙurin biya a nan gaba.

Gwamna Bago ya ce jihar na shirin biyan Naira miliyan ɗaya a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata.

Gwamna Bago zai biya mafi karancin albashi
Gwamna Bago ya ce Neja za ta iya biyan mafi karancin albashi na N1m a nan gaba Hoto: Umaru Muhammad Bago
Asali: Facebook

Gwamna Bago ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a gidan gwamnati dake Minna inda ya bayyana sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatan jihar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahu, ya bayyana sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago zai biya N1m nan gaba

Gwamna Bago ya nuna cewa da irin ci gaban da ya samu a harkar noma, jihar za ta biya ma’aikatan gwamnati Naira miliyan ɗaya a matsayin mafi ƙarancin albashi.

"Wannan abu ne wanda za mu iya. Za mu iya biyan N80,000. Muna da tabbacin cewa bisa nasarorin da muka samu a ɓangaren noma za mu iya biya."
"Mun ƙirƙiri gonar ma'aikata ta yadda ma'aikatanmu za su zama masu amfani. Da wannan, muna da tabbacin cewa za mu iya biyan Naira miliyan ɗaya a matsayin mafi ƙarancin albashi."

- Gwamna Umaru Bago

Yaushe zai fara biyan mafi ƙarancin albashi?

Gwamnan ya ba da tabbacin cewa sabon mafi ƙarancin albashin da ya amince da shi zai shafi ma'aikatan gwamnati jiha da na ƙananan hukumomi.

Ya kuma ƙara da cewa za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ne daga watan Nuwamba domin an riga da an biya albashin wannan watan na Oktoba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zama na farko a Arewa da ya amince da N80,000 a matsayin sabon Albashi

Gwamnati ta yi hatsaniya da ƴan ƙwadago

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu wata ƴar hatsaniya a lokacin bikin ranar malamai ta duniya na 2024 a cibiyar taro ta Mai shari'a Idris Legbo Kutigi da ke a jihar Neja a ranar Asabar, 6 ga watan Oktoban 2024.

Babban darakta na cibiyar bunkasa ilimi ta jihar Neja, Dakta Mustapha Ibrahim Lemu, ya yi watsi da korafe-korafen jin dadin malamai da 'yan kwadago suka gabatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng