Ndume: Lokutan da Sanatan APC Ya Jawo Hankalin Tinubu Ya Gyara Salon Mulki

Ndume: Lokutan da Sanatan APC Ya Jawo Hankalin Tinubu Ya Gyara Salon Mulki

Abuja - Mohammed Ali Ndume ‘dan siyasa ne maras tsoro, wanda ko kadan bai shakkun fadan abin da ya yi imani da shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Sanata Mohammed Ali Ndume ya na cikin jagorori a jam’iyyar APC mai mulki, amma ya saba fitowa ya soki gwamnatinsu.

Abin da rahoton nan ya yi shi ne kawo jerin lokutan da aka ji Sanata Ali Ndume ya na jan hankalin shugaban kasa Bola Tinubu.

Ali Ndume
Sanata Ali Ndume ya saba sukar Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Lokacin da Ali Ndume ya soki Tinubu

1. Ndume: An katange Bola Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu bai jima a Aso Villa ba aka ji Ali Ndume ya na zargin cewa wasu na kusa da madafan iko sun kudundune shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

Sanatan ya fadawa duniya cewa wasu manya sun hana Tinubu ganawa da jama’a, sai dai bai kama sunan wadanda suka yi shamakin ba.

This Day ta rahoto labarin, wanda daga baya APC ta maidawa Sanatan martani.

2. Tsadar rayuwa

Channels ta rahoto Sanatan ya na mai kira ga gwamnati ta yi kokarin rage tsadar rayuwan da mafi yawan ‘yan Najeriya suke kuka da shi.

A hira da aka yi da shi a gidan talabiji, duk da APC ta ke kan mulki, Ali Ndume ya nuna takaicin yadda kaya suka yi tashin gwauron zabi.

A halin yanzu kaya sun tashi a kasuwa, wannan ya jawo aka yi zanga-zanga a baya.

3. Matsalar rashin tsaro

Legit ta tuno lokacin da ‘dan majalisar ya soki yadda aka gagara kashe ‘yan bindigan da suka fitini al’ummar jihohin Arewacin Najeriya.

Ndume ya ba da misalin yadda aka murkushe Boko Haram, ya bukaci a dauko sojojin kasashen waje domin a gama da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wata magana, ya roki ƴan Najeriya su ci gaba da yi wa Tinubu addu'a

Daga baya sojoji sun tanka shi, suka nuna masa shawarar da ya kawo ba mafita ba ce.

4. Tallafin man fetur

Bayan fetur ya kara tsada har NNPCL ta maida farashin lita sama da N1000, ‘dan siyasar ya yi maza ya fito ya yi kira ga shugaban kasa.

‘Dan majalisar ya nunawa gwamnatin APC akwai bukatar a sauko da farashin fetur, a maganarsa, ya wanke shugaba Bola Tinubu daga zargi.

Punch ta ce Ndume ya yi ikirarin mashawarta ne suke neman kai Tinubu su baro.

Ndume da sukar gwamnatin Bola Tinubu

Ana da labari cewa sukar gwamnatin Bola Tinubu ne ya jawo Muhammad Ali Ndume ya rasa matsayinsa a majalisar dattawa a shekarar nan.

Bayan 'dan siyasar, akwai jerin tsofaffi da 'ya 'yan APC har gobe da aka ji sun soki gwamnatin Bola Tinubu saboda kuncin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng