'Ba Su Ya Kamata a Sallama ba,' Malami Ya Gano Kuskuren Tinubu a Korar Ministoci

'Ba Su Ya Kamata a Sallama ba,' Malami Ya Gano Kuskuren Tinubu a Korar Ministoci

  • Primate Elijah Ayodele ya yi ikirarin cewa ba a kori ministocin da ke kara jefa ‘yan Najeriya a cikin matsayin rayuwa a kullum ba
  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya bayyana cewa an ba Shugaba Bola Tinubu gurguwar shawara a korar ministoci
  • A cikin wata sanarwa, Primate Ayodele ya dage cewa ‘yan Najeriya za su yi murna ne kawai idan aka tsige gurbatattun ministoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya ce ba an ba Shugaban Bola Ahmed Tinubu gurguwar shawara kan korar ministoci biyar.

Bayanin babban malamin addinin Kiristan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Oluwatosin Osho ya fitar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara korar wasu ministoci daga aiki

Malamin addini ya yi magana kan korar ministoci da Bola Tinubu ya yi
Primate Ayodele ya ba Tinubu shawarar ministocin da ya kamata ya kora. Hoto: @primate_ayodele, @officialABAT
Asali: Facebook

Malami ya gano kuskuren Tinubu

A cikin sanarwar, Primate Ayodele ya dage cewa shugaban ya sauke ministocin da ba su ya kamata a ce ya sallama daga aiki ba, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya bayyana cewa yiwa majalisar minisstoci garambawul da Tinubu ya yi a ranar Laraba, 23 ga Oktoba, ba zai yi wani tasiri mai kyau ba

Primate Ayodele ya cehar sai Shugaba Tinubu ya sallami wadanda suka kamata daga aiki gwamnatinsa ne garambawul din zai haifar da da mai ido.

'A sallami wasu ministocin' - Malami

Da yake karin haske, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya za su yi murna tare da jinjina wa Shugaba Tinubu idan ya kori wasu ministoci, amma bai ambaci wani minista ba.

A cewar Primate Ayodele:

"Ba a canza ministocin da ya kamata a canza ba, wadanda aka canza ba za su iya kawo wani sauyi a gwamnatin mai ma'ana ba.

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

"Ya kamata a tsige ministocin da suka kallon kansu tamkar wasu Allan Musuru, wadanda komai sai da su za a yi. Su ne ya kamata a canja."

Jaridar New Telegraph ta tabbatar da jawabin Primate Ayodele a cikin wallafar da ta yi ranar Juma'a.

Tinubu ya ba ministoci sabon umarni

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya su rage motocin da ke cikin ayarinsu.

Shugaban kasar ya kuma umarci ministoci da shugabannin hukumomin su rage yawan jami'an tsaronsu zuwa jami'ai biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.